Gwamnan jihar kano Alhaji Abba kabir Yusif ya zubar da hawayen farin cikin a lokancin da yake mika yaran da aka sato daga jihar bauchi zuwa ga iyayen su.
Akalla yara takwas da aka sace yan rundunar yan sandan jihar Kano da hadin gwiwar ta jihar Bauchi suka gano.
A wata sanarwa da babban daraktan yada labaran gwamnan Kano Sanusi Bature Dawakin tofa ya aikowa kadaura24, yace gwamnan ya fashe da kuka ne a daidai lokacin da ya yake yabawa kwamishinan yan sandan jihar kano CP Husaini Gumai.

kimanin yara bakwai gwamnan jihar Kano ya sada su da iyayen su, ta hannun mahukuntan Gwamnatin jihar bauchi.
Sanarwar ta kara da cewa Gwamnan ya jinjina wa namijin kokarin rundunar ‘yan sandan jihar Kano, karkashin jagorancin CP Muhammad Hussain Gumel bisa wannan aiki.
Yanzu-Yanzu: Gwamnan Kano Abba Kabir Ya Sauyawa Ma’aikatar Mata ta Jihar Suna
Haka Kuma Injiniya Abba Kabir ya nuna matukar bacin ransa, duba da yadda aka kuma gano masu aikata laifin satar yaran daga arewacin najeriya suna safarar su zuwa jahohin anambra da legas dake kudancin kasar nan.
Gwamnan ya bukaci iyaye da su kasance masu lura da shige da ficen yaransu, domin Sauke nauyin da Allah ya dora musu.
Ana Ci-gaba Da Satar Yara Daga Arewa a Kaisu Kudancin Najeriya a Canza musu Addini da Yare
Ya kuma bukaci takwaran sa gwamnan jihar Bauchi, da ya dauki matakin shari’a akan wadanda ake zargin.
A nata bangaren gwamnatin jihar Bauchi,wadda daraktar sashen gabatar da kara na ma’aikatar shari’a ta jihar Barista Sha’awanatu Yusuf ta wakilta, tace gwamnatin jihar Bauchi za ta dauki matakan da suka dace na shari’a don ganin an gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu domin fuskantar hukunci.
‘Yan sanda a kano sun kama mutum 9 da laifin sayar da yara
Shima daya daga iyayen yaran da aka sace Malam Sa’ad, mahaifin Abdul mutallif Saad, ya bayyana godiyarsu ga gwamnatin jihar Kano dama kwamishinan ‘yan sanda na jihar.
A karshe gwamnan Kano ya bayar da gudun muwar kudi naira dubu dari biyar ga kowane yaran bakwai da aka gano.
Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito yadda Rundunar ‘Yan Sandan jihar Kano ta gano yaran bakwai, bayan wani aikin da suka gudanar, a tashar motar mariri dake jihar.