Daga Zakaria Adam Jigirya
Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar mazaɓar Kiru/Bebeji, Kano, Hon Abdulmumin Jibrin Kofa, a ranar Litinin ya ƙaddamar da ofishinsa na mazaɓa da za a yi amfani da shi wajen abubuwa uku a garin Kwanar Dangora da ke Karamar Hukumar Kiru, Kano.
Yayin ƙaddamarwar, ɗan majalisar ya yi bayanin cewa ginin, wanda za a riƙa amfani da shi a matsayin wani tsani tsakaninsa da mutanen mazaɓarsa, za kuma a riƙa amfani da shi wajen koyar da mata da matasan yankin sana’o’i da kuma koyar da na’ura mai ƙwaƙwalwa.

Hon Kofa ya kuma ce za a riƙa ayyuka ba kama hannun yaro kuma a kullum a cikin ofishin, kuma an ɗauki gogaggun ma’aikatan da za su riƙa kula da shi suna kuma karɓar koke-koken mutanen mazaɓar a madadinsa.
Kotu a Kano Ta Gargadi Khalid Ishaq Diso Game da Shugabancin Karamar Hukumar Gwale
Shugaban Ma’aikatan Jihar Kano kuma mai rikon mukamin Sakataren Gwamnatin Jihar, wanda ɗan asalin mazabar ɗan majalisar ne, Alhaji Abdullahi Musa ne ya ƙaddamar da ginin, yayin da ’yan Majalisar Dokokin Jihar Kano masu wakiltar mazaɓun Bebeji da kuma Kiru da sauran jagororin jam’iyya da dama ne suka taimaka masa yayin ƙaddamarwar.
Gabanin ƙaddamarwar, Hon Kofa ya kuma karɓi baƙuncin tsohuwar ’yar Majalisar Wakilan yankin, Hajiya Azumi Bebeji da ’yan Majalisar Kiru (Hon Usman Rabula) da na mazabar Bebeji (Hon Ali Tiga) da kuma shugabannin jam’iyyarsu a gidansa da ke Kofa, Bebeji.