Kotu a Kano Ta Gargadi Khalid Ishaq Diso Game da Shugabancin Karamar Hukumar Gwale

Date:

 

 

Babbar kotun jihar Kano ta hana Khalid Ishaq Diso gabatar da kansa a matsayin shugaban karamar hukumar Gwale.

Umarnin wucin gadi da alkalin kotun, Mai shari’a Aisha Ibrahim Mahmoud ta bayar, ya bada shi ne bisa bukatar da lauyan masu kara, Barista Bala Nomau ya gabatar a gaban kotun.

Talla

Kotun ta kuma hana Khalid Ishaq Diso da ma kowa daga gabatar da kansa matsayin shugaban karamar hukumar har sai an saurari karar da ke gaban kotu.

Yan sanda a kano sun kama mutum 9 da laifin sayar da yara

Tun da farko dai karamar hukukumar ta sanar da kotun cewa, kwamitin da majalisar dokokin jihar Kano ta kafa ya tsawaita wa’adin dakatarwar da aka yi wa Khalid saboda zargin amfani da matsayinsa yadda bai dace ba.

Wadanda suka shigar da karar su ne Ghali Nalele Bature da Ghali Umar Diso, yayin da wadanda ake karar sun hada da Khalid Ishaq Diso, ma’aikatar kananan hukumomi ta jihar Kano, da majalisar dokokin jihar Kano, da kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kano, da kuma karamar hukumar Gwale.

Kotun ta dage sauraren karar zuwa ranar 5 ga watan Junairu, 2024.

Aminiya

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Wata sabuwa: Sanata Barau Jibrin ya gana da Baffa Bichi da Muhd Diggol

Tsohon sakataren gwamnatin Jihar Kano Dakta Abdullahi Baffa Bichi...

Rikicin Masarautar Kano: Kotu ta Sake Sabon Hukunci

A wani sabon yanayi na rikicin Masarautar Kano, Kotun...

Gidauniyar Aliko Dangote za ta rabawa ‘yan Najeriya miliyan daya shinkafa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Gidauniyar Aliko Dangote ta raba buhunan...

Rufe Makarantu da azumi: Ministan Ilimi ba ta da ilimin harkokin mulki – Jafar Sani Bello

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Tsohon dan takarar gwamnan jihar Kano...