Daga Aliyu Danbala Gwarzo
Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf yace gwamnatinsa ta chanza sunan ma’aikatar mata ta jihar zuwa ma’aikatar mata yara da masu bukata ta musamman ta jihar kano.
” Ina so ku sani cewa wannan gwamnatin ta damu da ku, shi yasa tun da muka zo muka chanza sunan wannan ma’aikata kuma mun fara gyaran gidajen masu bukata ta musamman a jihar kano, Inda muka fara da gidan masu tabin kwakwalwa dake tudun maliki”.

Gwamna Abba Kabir ya bayyana hakan ne yayin taron bada tallafi ga masu bukata ta musamman 2,000 a kano domin su dogara da kawunansu, wanda aka gudanar a gidan gwamnatin jihar.
“Chanza sunan ma’aikatar matar zai taimaka waje sake matso da ku cikin gwamnati, sannan duk abun da za’a yi baza a manta da ku ba, zaku ma cigaba da amfanar wannan gwamnati in Allah ya so”. Inji Abba Kabir
Mataimakin Shugaban Kasa ya Bude Ofishin gwamnan Kano Da Aka Sabunta
Gwamna Abba Kabir yace gwamnatin sa ta bada mukamai daban-daban ga masu bukata ta musamman, kuma yayi alkawarin kara bada wasu mukaman don masu bukata ta musamman su tabbatar gwamnatin bata manta da su ba.
Gwamnan dai ya yi alkawarin cigaba da bujiro da aiyuka da tallafin da zai shafi masu bukata ta musamman kai tsaye da su da kuma ‘ya’yan su.