Daga Rahama Umar Kwaru
Mataimakin Shugaban Nigeria Kashim Shattima ya jagoranci bude ofishin Gwamnan Kano da aka sabunta dake gidan gwamnatin jihar.
Da yake bude ofishin, wanda gwamnatin jihar Kano ta sabunta, mataimakin shugaban kasa Kashim Shattima ya jinjinawa Gwamnan Kano bisa ayyukan raya kasa da yake aiwatar wa al’ummar a jihar.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da babban daraktan yada labarai na gwamnan Kano sanusi Bature Dawakin tofa ya aikowa kadaura24.

Rahotanni sun bayyana cewa Kashim Shatima ya zo jihar Kano ne, domin halartar jana’izar tsohon shugaban majalisar wakilan Nigeria marigayi Ghali Umar Na’abba, wanda aka yi jana’izarsa da yammacin Jiya Laraba.
Hotunan yadda akai Jana’izar Tsohon Kakakin Majalisar Wakilai Ghali Na’Abba
Haka kuma Kashim Shatima ya miƙa saƙon ta’aziyya ga gwamnatin Kano da iyalan mamacin a madadin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tunubu, inda ya bayyana mutuwar a matsayin babban rashi wanda baza’a iya mantawa da shi ba, bisa mahimmancinsa ga al’umma.
A yayin bude ofishin gwamnan, da kuma zuwa ta’aziyyar mataimakin shugaban ƙasar ya sami rakiyar mataimakin shugaban majalisar Dattijai Barau Jibrin, da sanatan Kano ta Kudu Abdurrahman Kawu Sumaila, da wasu ƴan majalisar tarayyar Najeriya.