Ku tabbatar da sahihancin labaran Socal Media kafin ku yada — Kabiru Idris

Date:

Daga Sani Magaji Garko

Kwararren Malami a sashen koyar da aiki jarida na kwalejin fasaha ta Polytechnic da ke nan Kano ya ja hankalin alumma musamman masu amfani da kafofin sada zumunta na zamani wato (Social Media) da tabbatar da sahihancin labari kafin su yada shi.

Malam Kabiru Idris Muhammad ya bayyana hakan ne a zantawarsa da manema labarai.

Ya ce sau da yawa wasu na kirkirar shafin internet (Website) domin yada labaran karya Wanda kuma labaran suna da matukar hatsari da barazar ga zaman lafiya da tsaro da kuma kasancewar Nigeria a matsayin kasa daya dunkulalliya.

“Ba kowanne labari ba ne yake labari, yakamata mutane su rika tantance labarai kafin su sanar da shi ko kafin su yada, saboda ba kowa kawai daga mutum yaji ko ya ga labari a social media ba zai yada”.

“Wasu mutane da yawa sun tafi kurkuku saboda labarin da suka yada a social media saboda ba Gaskiya bane, kaga kenan akwai bukatar kowanne mutum zai yada labari, ya tabbatar da sahihancin sa”.

Dangane da matsalolin da masu sayar da jaridu kan fuskanta sakamakon zuwa kofofin yada labarai na Internet, Malam Kabiru Idris Muhammad ya ce yanzu masu sayar da jaridu a kan hanyoyin na fuskantar barazanar rasa ayyukan su sakamakon canza harkokin karatun labarai daga bugaggun jaridu zuwa Wanda ake bugawa a shafin internet.

Ya ce akwai bukatar masu sayar da jaridar su sauya harkokin su zuwa na zamani idan akwai yuwuwar hakan domin cigaban kasuwancinsu.

8 COMMENTS

  1. Ya gyara tsakaninsa da dalibansa sanan yamana managa. Bashida kyakyawan mu’amala tsakaninsa da dalibai. Bai chanchanta abashi koyarwa ba.
    Masu tausayi da tunanin mai kyau ake bawa koyarwa.

  2. Hmm zubaida kenan gskiyane tunda bai zubar da mutuncinsaba, ya kame kansa daga sharrinku,kun fison ai ta washe muku Baki ,ana bude muku office , Allah sarki duniya Inka nuna kamun kai sai kafa wasu na jifan ka da Kalmar girman kai, mlm mutumin kirkine Kuma bashi da record din lalata ga duk wata daliba,kedai Allah ya shiryi irinku masu halin ,,,,

  3. Nigerian academic system has become corrupt so much that when a lecturer isn’t accommodating to the so called frivolous students like you he/she never seem to be good in the eyes of the myopic thinkers amongst you.
    Nonetheless, social media has given mindless people like you the utmost opportunity to post nonsense without consent!… I just hope you know you’re not in the position whatsoever to say this.
    I’d kindly advice you to focus on your studies not this coz you need that so much to make a difference, otherwise you’re in vain

    • Tell her d truth, she deserves not be going to sch, bcs, there’s no any plausible impact on her being a student, it’s quite incontestable that ,there only dearest wish is to sale their body to an irresponsible lectures whom they’re backing them up. if not u with your imbecility, how can on earth call someone who deserve to be as old as your father that he should redress the way his affairs with his student, if not u an insolent Ashawo, goal digger.

  4. Gaskiya ne abinda Zubaida ta fada ya gyara alakar shi da dalibai, wlh bashida mu’amala kwata kwata gashi bashida tausayi…. Wadanda ke defending dinshi dinnan da alama dai basu sanshi bane.

    • Hmm kune Baku sanshiba tunda ku burinku bai wuce ai iskanci da ku abaku maki ba, mu da mukai lami lfy Kuma ynxu muke aiki me ya taba hadamu dashi, kawaii system din karatunne ya lalace in har mlmi yasan abinda yake baxaita ba lalata da yard wani ba, Dan Shima Yana da yaya da kanne, ku Kuma burinku iskanci don gidan ya gagareku xama,shi yasa kuke xuwa college domin tallata hajarku,to mlm ba irinsu bane ,Dan zaran ba kalar yadin bane, da alama ma ku ko turanci ba ku iya ba Dan Dan reply din ma da Ake ba ku iyaba ,Aiko dole ku Samu matsala da mlm domin shi mlamin turancine Kuma baya harka da dakikai, irinku

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi Dangote ya sake rage farashin man fetur a Nigeria

Daga Rahama Umar Kwaru   Matatar mai ta Dangote ta bayyana...

Akwai bukatar kebe rana ta musamman a matsayin ranar tsofaffin dalibai a Kano – Kwamared Waiya

Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida, Kwamared Ibrahim...

Dubun wani magidanci da ke da’awar bin mamata bashi a Kano ta cika

Daga Aminu Gama   Kotun shari'ar musulunci da ke zamanta a...

Abubuwan da aka tattauna tsakanin Peter Obi da Gwamnan Bauchi Bala Muhammad

Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi ya ce a...