Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Dauda Kahutu Rarara, fitaccen mawakin siyasa na jam’iyyar APC, ya bukaci magoya bayan jam’iyyar da APC da su yi shirin yin murna cikin kwanciyar hankali da lumana, idan kotun ƙoli ta tabbatar da Dr. Nasiru Yusuf Gawuna a matsayin gwamnan jihar kano.
” Mu mutanen mu masu son zaman lafiya ne ba masu son tada hankalin jama’a ba, don haka Ina kira ga yan jam’iyyar APC da su yi murna cikin kwanciyar hankali ba tare da yiwa kowa komai ba, domin mai nasara baya fada”.
Kadaura24 ta rawaito Rarara ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da yayi da manema labarai a kano, dangane da hukuncin da kotun koli zata yanke kan zaben gwamnan jihar Kano da aka shirya yi a watan Disamba.

Rarara ya bayyana muhimmancin tallafawa hukumomin tsaro, musamman ‘yan sandan Najeriya, wajen wanzar da zaman lafiya a jihar, Inda yace yan sanda da sauran hukumomin tsaro suna aiki tukuru domin tabbatar da zaman lafiya.
Da yake jaddada bin doka da oda na ‘ya’yan jam’iyyar APC, Rarara ya bukaci ‘yan jihar da su bayar da tasu gudunmawar wajen samar da zaman lafiya idan kotun ƙoli ta yanke hukunci .
Na yi Nadamar Gudunmawar da Baiwa Gwamnatin Buhari – Mawaki Rarara
Rarara ya tunatar da al’ummar Kano cewa lokacin da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ta bayyana jam’iyyar NNPP a matsayin wadda ta lashe zaben gwamna da ya gabata , sun yan jam’iyyar APC basu tada hankali ha, sai suka tafi kotu domin ƙalubalantar nasarar.
Ya ce gwamnatin APC a lokacin ta bi doka, inda ta mika mulki ga dan takarar jam’iyyar NNPP. Bayan haka, APC ta bi hanyoyin doka, inda ta kalubalanci nasarar da NNPP ta samu a kotun sauraron kararrakin zabe.
“Ni ba wanda ya Isa ya ce ni ba Dan Kano ba ne domin matana biyu duk yan Kano ne, ‘ya’yana 9 duk a Kano na haifesu don haka dole na so zaman lafiyar jihar naso cigaban ta don haka ma ni sunana Dauda Adamu Abdullahi Kano”.
” Yadda mukai murna a gidajen mu ta hanyar yin addu’o’i lokacin da kotun sauraren kararrakin zaben gwamnan kano ta tabbatar mana da nasara haka mukai da kotun daukaka kara ta kara tabbatar mana da nasara, to amma idan kotun ƙoli ta sake tabbatar mana da nasara zamu yi murna mu zaga gari amma cikin kwanciyar hankali da lumana”. A cewar Rarara
Yayin da hukuncin kotun koli ke gabatowa, jam’iyyar APC na karfafa gwiwar ‘ya’yanta da su rungumi zaman lafiya, tare da karfafa imanin cewa zaman lafiya shi ne babban abin ci gaba da ci gaba.