Gabanin hukuncin da kotun koli zata yanke kan zaben gwamnan jihar Kano, rundunar ‘yan sandan Najeriya reshen jihar Kano, ta sake shan alwashin daukar kwararan matakai kan duk wata zanga-zanga da aka shirya da kuma duk wani abu da zai kawo cikas ga zaman lafiya da ake da shi a jihar.
Kwamishinan ‘yan sandan, Muhammad Usaini Gumel ne ya bayyana hakan yayin da manyan jam’iyyun siyasa biyu, NNPP, da APC, suka sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a Kano.

Jaridar Kadaura24 a ta ruwaito cewa, ana zaman dar-dar a Kano, yayin da mazauna garin ke jiran hukuncin da kotun koli zata yanke kan zaben gwamna mai cike da cece-kuce.
Kwamishinan ya yi nuni da cewa, kwamitin tsaron hadin gwiwa na jihar ya a shirye yake domin tabbatar da cewa duk wanda ya sabawa yarjejeniyar zaman lafiya da aka rattabawa hannu, to kuka da kan sa.
Nasiru Gawuna zai mayar wa yan kasuwar Kano wuraren su da aka rushe musu, in an gama Shari’a – Aruwa
Kwamishinan ‘yan sandan ya nuna bacin ransa kan yadda wasu kungiyoyi suke kokarin karya yarjejeniyar zaman lafiya a kwaryar birnin Kano.
“Ba za mu bar kowa, ko mi matsayinsa a cikin al’umma ya haifar da tashin hankali a Kano ba, domin mutanen Kano masu son zaman lafiya ne,” in ji shi.
Da yake jawabi, Shugaban Jam’iyyar NNPP na jihar kano, Hashimu Dungurawa da Mataimakin Shugaban Jam’iyyar APC na jihar, Shehu Maigari, sun sami sabani a kan wanda ya yake da alhakin abin da ya faru bayan rattaba hannu na farko da na biyu na yarjejeniyar zaman lafiya a jihar.
Hashimu Dungurawa, shugaban NNPP na jihar, ya zargi ‘yan jam’iyyar APC a matsayin masu tada zaune tsaye, ya ce jam’iyyarsu da kuma gwamnan jihar Alhaji Abba Kabir Yusuf suna aiki tare da jami’an tsaro domin tabbatar da zaman lafiya.
Sai dai mataimakin shugaban jam’iyyar APC, Shehu Maigari, ya ce kowa ya san wanda ke da alhakin tashe-tashen hankula da zanga-zanga a jihar, inda ya ce jam’iyyarsu ba ta da wata damuwa.