Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Isma’il Muhammad, Shugaban Kungiyar bunkasa tattalin arziki a Inda aka sami sarkakiya tsakanin al’ada da addini yace rushe masana’antar Kannywood ba zai kawo ƙarshen aikatawa ko yaduwar badala a cikin al’umma.
” Kannywood ta fara tsaiwa da kafarta ne Shekaru 20 da suka gabata, Kuma ba wanda ya Isa yace a wancan lokacin ba’# aika ta badala, don haka Ina bada tabbacin cewa Kannywood ba ita ce ta Kawo badala cikin al’umma ba”. Inji Isma’il Muhammad
Isma’il Muhammad ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da yayi da wakiliyar jaridar kadaura24 a Kano.
Yace a jami’o’in kasar nan ana gudanar da badala wacce ko kamar kafar Kannywood bata kai ba, amma abun mamaki shi ne yadda ba’a ganin abun da ake yi a wadancan jami’o’i sai masana’antar Kannywood wadda ta ke baiwa take bawa matasa sama da Miliyan 1 aikin yi a Arewacin kasar nan.
A cikin fim ne kadai ake iya gane kasar da ta samu cigaba saboda baka d Wani hanya da zaka iya yin magana d duniya idan ba t hanyar fina-finai ba. Ko kasashen d suka ci gaba suna tunkaho d masana’antun fina-finan kasashen su.
” Babu shakka mun yarda akwai kura-kurai a harkokin da ake a Kannywood, amma bai kamata ace saboda ana samun kura-kurai ace yiwa harkar kuɗin goro ba, ta hanyar muzanta sana’ar, bayan kowa yasan a kowacce sana’a akwai hanyar da zaka bi ta kai ka aljanna ko wata to haka ita ma Kannywood ta ke”.
Yanzu-Yanzu: Gwamnan Kano Abba Kabir ya nada sabon shugaban ma’aikatan jihar
Isma’il Muhammad ya bada shawara ga gwamnati domin tsaftace harkar fim din, Inda ya ce kamata yayi gwamnati ta rika tura wakilanta duk Inda za’a ɗauki fim domin wakilan su rika sanya idanu kan abubuwan da ake yi na ba dai-dai ba, domin gyarawa.