Daga Rukayya Abdullahi Maida
Mataimakin gwamnan jihar kano Kwamarat Aminu Abdulsalam Gwarzo ya bukaci yan jaridu da jama’an yada labarai su rika rungumar sauyin da ake samu a faggen yada labarai koda yaushe.
Cigaban da ake samu mai dauke da kalubale da yawa a aikin jarida ke kawo barazana ga ma’aikata, don haka nake kira ga duk wani jami’in yada labarai tun daga matakin farko a karatu zuwa makura, ko wadanda suka dauki tsawon shekaru a aikin, wajibi su yadda cewa fagen aikin yada labarai fage ne dake zuwa da sabon ilimi a Koda yaushe”.

Mataimakin Gwamnan jihar kano kwamarad Aminu Abdul Salam Gwarzo shi ne ya bayyana haka yayin bitar kwanaki shida da ma’aikatar yada labarai ta shirya ga jami’anta na kanan hukumomi 44 a jihar Kano.
Kwamarad yace Akwai bukatar jami’an yada labarai su zama masu bibiya, karance-karance, shiga shafuka da kuma halartar bita don karawa Juna sani domin su inganta aikinsu, jin ilimi ya ishi mutum ko gadara da dadewa cikin aikin zai iya sawa a bar mutum a baya .
Tinubu ya naɗa sabbin kwamishinonin zaɓe a jihohi tara
Wasu Daga Cikin mahalarta bitar daga wasu kananan hukumomin sun bayyana gamsuwa da abubuwa da aka koya musu kan sha’anin yada labarai, daga bisani suka mika godiyarsu ga gwamnan jihar kano dama kwamishinan yada labarai daya jajirce wajen tabbatar da wannan bita.
Dayake jawabi kwamishinan yada labaran da harkokin cikin gida na jihar Kano, Baba Halilu Dantiye MON MNI, ya shaida cewa yana da yakinin jami’an da aka baiwa bita zasu kara inganta aikinsu don dama sun iya, sannan kashin farko ne suka kammala inda aka kawo kwararrun masu bada horo a fannoni daban – daban.
Dan tiye ya tabbatar da cewa za suyi kundi su mayar da da duk takardun da aka gabatar Littafi Domin ya zama tarihi ga Mutane Baya, don su ma su amfana .

kwamishina yace baya ga jami’an yada labaran, gwamnatin jihar kano zata shirya irini wannan bita ga masu bada rahoto na musamman da Gwamna ya dauka, da ma’aikatan radio na gwamnati da masu zaman kansu don kara inganta harkokin yada labarai a jihar kano.
Kimanin jama’ai yada labarai 214 ne rukunin farko suka rabauta da bitar daga ofisoshin yada labarai na kanan hukumomi 44, da ma’aikatar yada labarai baki daya kamar yadda Gwamnan Kano Eng. Abba Kabir Yusuf ya dauki nauyi.