An bayyana gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano matsayin Shugaban da ya taba rayuwar al’umma musamman a cikin kwanaki Dari da yayi a karagar mulkin sa na matsayin gwamnan Kano.
Wannan na zuwa ne daga bakin daya cikin masu kishin cigaban jihar Kano Kuma jigo a jam’iyyar NNPP a jihar wato Hon Aminu Aminu Mai Famfo a wata zantawa da yayi da manema labarai ranar lahadi.
Mai Famfo Wanda ya kasance daya daga cikin wadanda suka bada gagarumar gudunmuwar da ta taba rayuwar al’umma daga jihohin kasar nan ta hanyar tallafi da sauran ayukan raya marassa karfi a lokuta da yawa.
Hon Aminu ya tabbatar da cewa yazuwa yanzu wasu daga cikin ayukan da Mai girma gwamna Abba Kabir Yusuf yayi sun canza akalar jihar Kano ta fuskoki daban-daban.
Mai Famfo ya ce kamar Kwato asibitin Yara na Hasiya Bayero da gwamna yayi na daga cikin ayukan da baza’a taba mantawa da namijin kokarin sa duba da yadda tsohuwar gwamnatin da ta gabata,wadda ta sallama ma wani daga cikin jami’anta cikin farashi mai rahusa.
Barazanar kisa: NBA ta yabawa Gwamnan Kano, ta bukaci jami’;an tsaro su fara bincike
Hon Aminu Aminu ya Kuma bayyana gyaran fitulun kan tituna da cigaba da aikin titin Wuju-Wuju Hadi da cigaban titunan kananan Hukumomi 44 da tsohuwar gwamnati jagorancan Kwankwassiya Dr.Rabiu Musa Kwankwaso tafara ta kammala ba Mai tsawon Kilometer biyar-biyar na da matukar mahimmanci a ayukan raya karkara.
Bayan wadannan ayukan Kuma akwai batun gyaran titunan cikin birni da hukumar karma ke yi tare da shirin auren gata na mutum kimanin dubu biyu (2000)da Mai girma gwamna ya bada umarni gabatarwa nan bada jimawa ba.
“A kan abinda mu ke na tallafama masu karamin karfi daga lokutan baya yazuwa lokacin yakin neman zabe,to yanzu nasan wannan tallafi zai ninka saboda irin tunanin da Mai girma gwamna Abba Kabir yake dashi na taimakama masu karamin karfi.”
Aminu Mai Famfo ya kuma bukaci magoya bayan gwamna Abba Kabir da jam’iyyar NNPP da sauran al’ummar jihar da su cigaba da gudanar da addu’o’i dan samun nasara a shari’ar da take gudana a kotu yanzu domin cigaba da ayukan alkhairi ga Jama’ar Kano kamar yadda yayi alkawari lokacin yakin neman zabe