Yadda wani Mahaifi ya kashe jaririyar kwana ɗaya da haihuwa saboda ya fi son ɗa namiji

Date:

 

Wani matashi dan shekara 28, mai suna Misbahu Salisu, ya kashe jaririyar da aka haifa masa, kwana ɗaya da haihuwa, saboda ya fi son ya samu da namiji.

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ce ta kama mutumin da ke zaune a Doka Baici a karamar hukumar Tofa a ranar Juma’a.

 

Hukumar ta sanar da kama shi ne a cikin wata sanarwa da mataimakin kwamandan rundunar ɓangaren sintiri Mujahid Aminudeen ya fitar a Kano.

Talla

Aminudeen ya ce wanda ake zargin ya sanar da jami’an hukumar cewa ya bai wa jaririyar fiya-fiya shine ta rasu.

Yanzu-Yanzu: Tinubu ya sake nada sabbin ministoci guda 2

Salisu ya kuma baiwa mahaifiyar jaririyar mai suna Sa’ade kwaya a ciki shayi, inda bacci ya kwashe ta kafin ya aikata laifin.

 

“Wanda ake zargin ya amsa laifinsa, inda ya ce ya fi son ɗa namiji ne amma matarsa ​​ta haifi mace, wanda hakan ya sa ya kashe jaririyar,” in ji jami’in a cikin sanarwar.

Ya ce an mika wanda ake zargin ga ‘yan sanda domin gudanar da bincike da gurfanar da shi gaban kuliya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kungiyar ’Yan Jaridun Kano Arewa ta Aike da Sakon Ta’aziyyar Rasuwar Alhaji Aminu Dantata

  Kungiyar ’Yan Jarida ta Kano Arewa ta bayyana alhinin...

Ku na da rawar takawa wajen inganta Lafiyar al’ummar Kano – Waiya ga jami’an yada labarai

Daga Abubakar Sayeed Kwamishinan Ma'aikatar yada labarai da harkokin cikin...

Ana daf da yin jana’izar Aminu Dantata a Madina

Tawagar da gwamnatin Najeriya ta tura zuwa Madina na...