Daga Rukayya Abdullahi Maida
kwamishinan ilimi na jihar Kano, Umar Haruna Doguwa, ya bayyana cewa yanzu haka ɗaliban makarantun firamare a jihar sun kai miliyan 5 da dubu dari 2, inda kusan miliyan 4 daga cikinsu suke zaune a kasa sakamakon rashin wadataccen kujera da kayan aiki.
Kwamishinan ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi a shirin “A Fada A Cika” na BBC Hausa, wanda aka shirya da nufin zaburar sabbin masu rike da mukaman siyasa su mayar da hankali wajen cika alkawuran da suka yi yayin yakin neman zabe.
Alkaluman da kwamishina Doguwa ya fito da su, sun nuna kalubalen da ilimi a jihar Kano ke fuskanta, wanda ke fama da dimbin daliban da suka zarce yawan kayan koyo da koyarwa da ake da su a jihar. Mummunan halin da ake ciki ya haifar da damuwa game da ingancin ilimi da kuma jin dadin wadannan dalibai.
Yanzu-Yanzu: Tinubu ya sake nada sabbin ministoci guda 2
Da yake amsa tambayoyin masu sauraro game da tabarbarewar ilimi a Kano, Umar Haruna Doguwa ya amince da cewa ya zamar musu dole su dauki matakan gaggawa domin magance wannan matsala. Ya kuma bayyana bukatar gaggauta daukar matakan da suka dace domin inganta harkar ilimi ga matasan Kano, inda ya jaddada cewa kowane yaro ya cancanci samun ingantaccen ilimi a yanayi mai Kyau .
Wannan tonon sililin ya haifar da sabon kira na kara saka hannun jari a bangaren samar da ababen more rayuwa a makarantun firamare don tabbatar da kyakkyawar makoma ga miliyoyin dalibai a jihar Kano. Yayin da gwamnati ke fama da wannan matsalar ilimi, ta mayar da hankali ne kan cika alkawuran da ta dauka na samar da ingantaccen yanayin koyo ga kowa.