Gwamnatin jihar Kano ta umarci jami’anta wadanda suka haɗar da kwamishinoni da masu baiwa gwamna shawara da dukkanin wani mai mukami a gwamnatin da ya guji yin kalaman da basu da nasaba da hukuma ko ma’aikatarsu.
Kwamishinan ma’aikatar yada labarai da harkokin cikin gida na jihar kano Baba Halilu Dantiye ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai ya gudanar a gidan gwamnatin kano.
Yanzu-Yanzu: Gwamnan Kano ya Kori kwamishinan kasa da mai bashi shawara kan harkokin Matasa
Kwamishinan yace Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya umarci dukkanin masu rike da mukamai a gwamnatinsa da su tabbatar duk maganar da zasu yi musamman a kafafen yada labarai tana da nasa ba da ma’aikatun da suke jagoranta .
” Idan harkar ma’aikatarka ce kana da dama kayi magana akai saboda kafi kowa saninta , Amma idan ba haka to sai ka nemi izini Kuma sai ka jira har an baka dama sannan sai ka yi”. Inji Baba Dantiye
Yace Kuma gwamnan ya jaddada cewa gwamnatin jihar kano bata sake lamuntar wani jami’inta ya yi kalamai na tunzura al’umma ba, Inda yace gwamnatin zata ɗauki matakin da ya dace akan duk wanda ya sabawa wanann umarni.
Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito a jiya gwamnan kano Abba Kabir Yusuf ya sallami kwamishinan kasa da safayo na jihar Adamu Aliyu Kibiya da mai bashi shawara kan harkokin Matasa da wasanni Yusuf Imam Wanda aka fi sani da Ogan Boye daga kan mukamansu, saboda kalaman tunzura al’umma al’umma da kuma barazanar kashe alkarai da sukai.