Kwana 100 Abba Gida-gida a Kano sun kara daga darajarmu – Zannan Kwankwasiyya

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

 

Zannan Kwankwasiyya, kuma daya daga cikin jagororin Jam’iyyar NNPP a yankin Karamar Hukumar Nasarawa Alhaji Abubakar Yahuza Gama, ya yabawa Gwamanan Jihar kano Alhaji Abba Kabir Yusif, bisa managartan ayyukan da ya samarwa Kanawa a kwana 100 da shigarsa Ofis.

 

Kadaura24 ta rawaito Alhaji Abubakar Yahuza Gama ya yi wannan yabo ne, cikin sakon taya murna da ya fitar, wanda ya rabawa manema labarai, da nufin tunatar da al’umma irin ayyukan raya kasa da gwamnan ya samar a kwana 100 da hawansa mulkin Kano.

Talla

Alhaji Yahuza Gama yace a Kwanki 100 da Karbar mulkin Jihar Kano, daga Hannun yan walawala Kanawa sun rabauta da Ayyukan ci gaban ƙasa.

Da dumi-dumi: Bayan korar karar Atiku, Kotun ta tabbatar da nasarar Tinubu

Daga ciki akwai biyawa Daliban Jami’ar Bayero kudin makaranta, su kimanin 7,000 tare da Rage Kaso Hamsin cikin Dari na kudin Makarantar dalibai yan asalin Kano dake karatu a manyan makarantun jihar.

Sannan akwai karasa Aikin Titin Wujuju, da gina shataletalen titin gidan Gwamnati, da dawo da shirin fitar da Ya’yan Talakawa Kasar waje domin karo ilimi.

Har ila yau a kwana darin Abba, akwai batun Samar da Ruwan sha a uguwannin da suka shefe Shekara da shekaru babu Ruwan Famfo, biyan Ma’aikata Albashi Akan Lokaci , tallafin Kayan Abinci ga Marasa Karfi da dai Sauran manyan Ayyuka.

Talla

Zannan ya kuma Kara da cewa Gwamman Jihar Kano ya yiwa Sauran Gwamnoni zarra a Fadin Kasarnan a iya kwanaki 100 da suka karbi Mulki.

A don haka ne Alhaji Abubakar Yahuza Gama yayi fatan ayyukan kwanakin gaba, zasu samar da gagarumin ci gaba ga al’ummar Kano da ma jihar baki daya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Wata sabuwa: Sanata Barau Jibrin ya gana da Baffa Bichi da Muhd Diggol

Tsohon sakataren gwamnatin Jihar Kano Dakta Abdullahi Baffa Bichi...

Rikicin Masarautar Kano: Kotu ta Sake Sabon Hukunci

A wani sabon yanayi na rikicin Masarautar Kano, Kotun...

Gidauniyar Aliko Dangote za ta rabawa ‘yan Najeriya miliyan daya shinkafa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Gidauniyar Aliko Dangote ta raba buhunan...

Rufe Makarantu da azumi: Ministan Ilimi ba ta da ilimin harkokin mulki – Jafar Sani Bello

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Tsohon dan takarar gwamnan jihar Kano...