Daga Aliyu Nasiru Zangon aya
Jam’iyyar Labour ta yi watsi da hukuncin da kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa ta yanke na tabbatar da Bola Tinubu na jam’iyyar APC, a matsayin wanda ya lashe zaben ranar 25 ga Fabrairu, 2023.
Sakataren yada labarai na jam’iyyar na kasa, Obiora Ifoh, ne ya bayyana matsayin jam’iyyar a Abuja, jim kadan bayan kotun ta bayyana hukuncin ta.

Ifoh ya ce, “Jam’iyyar Labour ta yi mamakin hukuncin da kotun sauraron kararrakin zaben Shugaban kasa wadda karkashin jagorancin Mai shari’a Haruna Tsammani ta yanke a yau kuma mun yi watsi da sakamakon hukuncin da aka yanke gaba daya saboda ba a yi adalci ba .
“’Yan Najeriya shaidu ne kan fashin zaben da aka yi a ranar 25 ga Fabrairu, 2023, wanda duniya ta yi Allah wadai da shi amma kotun a cikin hikimar ta ta ki amincewa da hakan.
Da dumi-dumi: Kotun zaɓen shugaban ƙasa ta kori ƙarar Peter Obi
“Abin da ake ciki shi ne an ci mutuncin dimokuradiyya kuma ba za mu yi kasa a gwiwa ba har sai jama’a sun sami nasarar da suke fata.
Muna jinjina wa tawagar lauyoyin mu da suka fallasa abun da aka yi mana ba tare da tsoro ba.
