Mun Cika duk Sharuddan da ECOWAS ta Gindaya Mana – Sojin Nijar

Date:

Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa

 

Firaministan Nijar da sojoji suka naɗa, Ali Lamine Zeine, ya ce ƙasarsu ta cika dukkan abubuwan da ƙungiyar Ecowas ta nema daga gare su.

 

“Abubuwan da suka nema su ne tattaunawa da Ecowas, da ganin shugaban ƙasa [Bazoum], da kuma saka lokacin da za a mayar da mulki ga farar hula,” in ji shi.

Da dumi-dumi: Kotun Sauraren Kararrakin Zaben Shugaban Kasa ta Bayyana Ranar da Zata Yanke Hukunci

Zeine ya bayyana haka ne yayin taron manema labarai da ya kira ‘yan mintuna da suka wuce a birnin Yamai, yana mai cewa amma har yanzu ba a cire takunkuman da aka saka musu ba

“Tsohon shugaban Najeriya da sarkin Musulmi sun zo nan sau biyu, manyan malamai ma sun zo. Kuna gani ni na raka su suka ga Bazoum.

Talla

“Sannan mun ce musu [wa’adin miƙa mulki] ba zai wuce shekara uku ba – saɓanin yadda ake faɗa a kafofin yaɗa labarai, ba shekara uku muka ce ba.”

Ya kira takunkuman da Ecowas – ƙungiyar raya tattalin arzikin ƙasashen Afirka ta Yamma – ta saka wa Nijar ɗin a matsayin “haramtattu” sakamakon juyin mulkin da sojoji suka yi a watan Yuli.

Ya bayyana cewa suna fatan nan da makonni masu zuwa za a cimma matsaya tsakanin sojojin mulkin ƙasar da kuma Ecowas.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Muna bukatar kayan aiki domin magance matsalar tsaro a karamar hukumar Nasarawa – Muhd Haruna Black

Kwamandan Jami'an sintiri na karamar hukumar Nasarawa a jihar...

Da dumi-dumi: An Sanya dokar Hana fita a Kaduna

Gwamnatin Kaduna ta sanya dokar taƙaita zirga-zirga ta tsawon...

Yanzu-Yanzu: An ɗage jana’izar Aminu Ɗantata saboda wasu dalilai

Gwamnatin Najeriya ta sanar da ɗage jana'izar fitaccen ɗankasuwar...

Kungiyar Farfado da martabar Arewa ta Mika sakon ta’aziyyar Rasuwar Aminu Dantata

Daga Sadiya Ahmad   Kungiyar Farfado da martabar Arewa ta Mika...