Daga Ibrahim Sani Gama
Gwamnatin jihar kano ta jaddada kudirinta na kara inganta harkokin ciyar da dalibai ‘yan makarantun firamare da sakandire a fadin jihar kano.
Umar Musa Gama yace ofishinsa zai yi iya kokarinsa domin ganin ya sauke nauyin da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya dora masa da kuma nauyin al’ummar jihar kano, musamman daliban Makarantu dake faraimare da sakandire.

Mai baiwa Gwamnan jihar kano shawara na musamman a fannin harkokin ciyar da dalibai Alh. Umar Musa Gama ne ya bayyana hakan a lokacin yake zantawa da manema labarai a ofishinsa.
Ganduje ya bayyana dalilan da suka sa Tinubu ya cire sunan Maryam Shetty daga cikin Ministocin
Yace ofishinsa ba zai amince wasu mutane su rika kai abinci mara inganci ba ko amfani da sauran kayayyakin masarufi marasa kyau ba,inda ya bada tabbacin yin duk mai yiyuwa don tabbatar da an baiwa dalibai abinchi Mai gina jiki da kara lafiya.

“Tun lokacin da mai girma gwamnan jihar kano Abba kabir Yusuf ya bani wannan mukami, na fara aiki ka’in da na’in domin ganin na sauke nauyin da ya rataya a wuyana, ina Kuma amfani da wannan dama wajen godewa jagoran kwankwasiyya kuma Tsohon Gwaman kano, Sanata Dr. Rabi’u Musa Kwankwaso da Gwamnan jihar kano, injiniya Abba kabir Yusuf, duba da yadda suka dubi cancantata suka bani wannan aiki, domin hidimtawa al’ummar jihar kano da daliban jihar kano domin kara habaka harkokin ilimi a jihar baki daya”. Inji Umar Musa Gama
Kwankwaso ya Taya Ganduje Murnar zama Shugaban APC na Ƙasa
A jawabansa Alh. Mamman nation Gama ya bayyana cewa gwamnan kano yayi hangen nesa bisa zakulo Danladi maggi, kuma an ajiye kwarya a gurbinta, inda kuma ya bukaci al’ummar jihar kano da su marawa umar musa gama baya domin samun damar sauke nauyin daya rataya akansa, musamman yawaita yin addu’oi samun nasarar ayyukansa yadda ya kamata.
Shi ma a jawabinsa,Alh.Yahuza Abubakar Gama, ya shawarci dukkannin ‘yan jam’iyya da ‘yan uwa da abokanan hulda da tayashi da Addu’oin samun nasara a wannan ayyuka da zai fara, sannan ya shgawarcin sabon S A na gwamna da ya kasance mai gaskiya da rikon amana kamar yadda suka san shi, domin hakan ne kadai zai ba shi damar hidimtawa al’umma yadda ya kamata.