Masu ruwa da tsaki sun bukaci hutun watanni 6 ga mata masu aiki domin shayar da jarirai nonon uwa zallah

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 

Masu ruwa da tsaki a fannin kiwon lafiyar mata masu juna biyu a jihar Kano, sun bukaci gwamnatin jihar da ta kara wa’adin hutun haihuwa da ake biya daga watanni uku zuwa shida a wani mataki na samar da kyakyawan yanayi ga uwa don shayar da jarirai zallar nonon uwa.

 

Shugaban tawagar, Alive and Thrive, Dokta Ashiru Hamza Muhammad shi ne yayi kiran a ranar Alhamis, inda ya ce baza a iya misalta muhimmancin shayar da jarirai nonon uwa ba, domin yana kara garkuwar jiki, da kuma kara lafiyar kwakwalwa ga yaran.

 

“Shayar da jarirai zallar nonon uwa a cikin kwanaki 1,000 na farkon rayuwar yara, shi ne gatan da zaki yiwa ‘yar ki ko dan ki domin ya samu lafiyar da zai iya bada ta gudummawar wajen ga ci gaban kasa.” Inji Dr. Muhammad.

Talla

Shugaban ofishin UNICEF a Kano, Rahama Farah, ya jaddada cewa kashi 9% na ma’aikatu ne ke da tsarin bada damar shayar da jarirai nonon uwa a wurin aiki, inda kashi 1.5% ne kacal a bangaren gwamnati.

Kwankwaso ya Taya Ganduje Murnar zama Shugaban APC na Ƙasa

Ya yi wannan kiran ne tare da sauran masu ruwa da tsaki da suka hada da mata masu shayarwa a Kano, a yayin wani taron karawa juna sani na wayar da kan masu ruwa da tsaki kan samar da kyakyawan yanayin shayarwa ga iyaye masu aiki, a wani bangare na taron shayar da nonon uwa na duniya na shekarar 2023 (WABA) a wani ɓangare na makon shayar da jarirai nonon uwa na wannan Shekarar, wanda aka shirya tare da hadin gwiwar Ma’aikatar Lafiya ta jihar kano da FHI360 Alive & Thrive.

Talla

Farah ya ce akwai bukatar a samar da yanayi cikin gaggawa inda za’a tallafawa iyaye masu aiki a kokari da suke yi na kula da ‘ya’yansu tare da kuma suna aikinsu.

Sojojin Nijar sun yi sabbin nade-nade

Ya ce baya ga kiran da ta yi ga gwamnatin jihar Kano ta tsawaita hutun haihuwa da ake biya daga watanni uku zuwa shida, kuma ya bukaci gwamnatin ta ba da fifiko ga bukatun iyaye masu aiki ta hanyar samar da dakunan shan nono a duk ma’aikatu da hukumomi, don baiwa jariransu kulawar data dace.

Ya kuma roki gwamnati “Ta samar da isassun kayan aiki don rigakafin cutar tamowa ta hanyar ingantawa, kariya da tallafawa wajen samar da abinci mai gina jiki na mata masu juna biyu, jarirai da kuma kananan yara.

“Ƙarfawa wajen aika saƙonni kan samar da ingantaccen abinci mai gina jiki da karin lafiya a cikin kwanaki 1,000 farko na rayuwar yara ta hanyar yin amfani da kafofi daban-daban, kamar irin su kafofin yada labarai, wuraren jama’a, da wuraren aiki zai taimaka matuka.” A cewar sa

Ya kara da cewa, “A karshe, kamar yadda yake shayar da jarirai nonon uwa hakki ne da ya rataya akan kowa, UNICEF tana kira ga kowa da kowa, musamman sarakunan gargajiya shugabannin addini, shugabannin al’umma, kungiyoyin farar hula, kafofin yada labarai, da kowa da kowa da su tallafa wajen aiwatar da tsarin shayar da jarirai nonon uwa zalla.”

Tun daga shekarar 1992, WABA take shirya tarukan wayar da kan al’umma da sauran masu ruwa da tsari kan kan muhimmancin shayar da jarirai nonon uwa a wani ɓangare na bikin Makon Shayar da Nono na Duniya .

Tun da farko a jawabinsa na maraba, kwamishinan lafiya na jihar Kano, Dakta Abubakar Labaran, wanda daraktan kula da lafiyar jama’a, Dakta Rajab Ashiru ya wakilta, ya ce hanya mafi inganci ta rigakafin cutar tamowa ga yara ita ce shayar da jarirai nonon uwa zalla.

Ya kara da cewa shayar da jarirai nonon uwa zalla na baiwa yaron kariya daga kamuwa daga kowace irin cuta kamar gudawa da sauransu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yanzu-Yanzu: An ɗage jana’izar Aminu Ɗantata saboda wasu dalilai

Gwamnatin Najeriya ta sanar da ɗage jana'izar fitaccen ɗankasuwar...

Kungiyar Farfado da martabar Arewa ta Mika sakon ta’aziyyar Rasuwar Aminu Dantata

Daga Sadiya Ahmad   Kungiyar Farfado da martabar Arewa ta Mika...

Kungiyar ’Yan Jaridun Kano Arewa ta Aike da Sakon Ta’aziyyar Rasuwar Alhaji Aminu Dantata

  Kungiyar ’Yan Jarida ta Kano Arewa ta bayyana alhinin...

Ku na da rawar takawa wajen inganta Lafiyar al’ummar Kano – Waiya ga jami’an yada labarai

Daga Abubakar Sayeed Kwamishinan Ma'aikatar yada labarai da harkokin cikin...