Shugabannin mulkin sojin Nijar sun gudanar da sabbin naɗe-naɗe a ƙasar.
Cikin wata sanarwa da sojojin suka fitar ranar Juma’a da daddare, sun sanar da naɗin Janar Moussa Salau Barmou a matsayin babban hafsan hafsoshin soji na kasar.

Sai kuma Kanal Amirou Kader a matsayin mataimakinsa.
Manjor Kanal Sani Kiaou shi ne sabon shugaban rundunar sojin ƙasa, in ji sanarwar.

Sai kuma Kanal Abdoutahamane Zataka a matsayin mataimakinsa.
Sanarwar ta kuma ce Janar Sani Kache ne sabon sakaren ofishin ministan tsaro na ƙasar.
Sojojin na Nijar dai sun ce a shirye suke su mayar da martani idan ƙungiyar Ecowas ta kai musu farmaki cikin ƙasarsu.