Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Matashiyar nan wadda shugaban kasa Bola Tinubu ya sanya sunanta cikin ministocinsa Maryam Shetty ta bayyana Rashin damu bisa yadda Shugaban kasa ya cire sunanta daga cikin ministocinsa.
” Yayin zaman majalisa a wannan rana ta juma’ar nan, na sami labarin cire sunana daga cikin wadanda Shugaban kasa Bola Tinubu zai nada a matsayin ministocinsa, tare da maye gurbina da Dr. Mahmoud Mairiga”. Inji Maryam Shetty

Maryam Shetty ta bayyana hakan ne a sashin shafinta na Twitter, jim kadan bayan sanar da cire sunanta daga cikin ministocin.
Yanzu-Yanzu: Tinubu ya sauya sunan Maryam Shetty daga Ministocinsa
” Ina matukar jin dadin da godiya da matakin da shugaban kasa ya dauka”. Inji Shetty
Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito cewa a zaman majalisar dattawa ta wannan rana ta juma’a Shugaban kasa Bola Tinubu ya aikewa majalisar da wasikar sauya sunan Maryam Shetty da Mariya Mahmoud Bunkure, bayan tura sunan a ranar laraba mai zuwa.
Har yanzu dai babu sashihin labarin dalilin da yasa aka sauya sunan Maryam Shetty daga cikin ministocin da Shugaba Tinubu zai nada.