Daga Safwan Suraj Iliyas
Shugaban kasar Nigeria Bola Tinubu ya aikewa majalisar dattawa sunan tsohon Ministan ƙwadago na kasa Festus Keyamo domin amincewa da shi don nada shi a matsayin minista.

Haka Kuma Shugaba Tinubu ya aike da sunan Dr. Mairiga Mahmud domin maye gurbin Maryam Shetty daga Kano wadda aka tura sunanta a ranar Larabar data gabata.
Tinubu ya aike da sunayen ne ta cikin wata wasika da ya aikewa majalisar dattawa kuma Shugaban majalisar Godswill Akpabio ya Karanta a zaman majalisar na yau juma’a.