Daga Maryam Ibrahim Abubakar
Wakilan kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka (ECOWAS) tsohon shugaban kasa Nigeria Janar Abdussalam Abubakar mai ritaya da mai alfarma Sarkin Musulmin Nigeria Muhammadu Sa’ad Abubakar sun isa birnin Yamai na Jamhoriyyar Nijar fadar mulkin kasar.
Wakilan kungiyar ta ECOWAS sun je kasar Nijar din ne domin lalubo bakin zaren yadda za’a warware rigingimun da ke faruwa a kasar, biyo bayan juyin mulkin da sojoji suka yi na hambarar da zababbiyar gwamnatin dimokuradiyya kwanaki kadan da suka wuce.

Ana sa ran manyan ‘yan Najeriyan biyu za su tattauna da shugabannin da suka yi juyin mulki a Kasar ta Nijar.
Wata sanarwa mai dauke da sa hannun Ajuri Ngelale – mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai ranar Alhamis, ta ce Tinubu ya aike da wakilai zuwa Yamai, kuma ya bukaci tattaunawa mai karfi don kawo karshen matsalar.
Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito a makon da ya gabata ne sojojin Kasar Nijar suka hambarar da gwamnatin farar hula ta ƙasar wadda ke karkashin jagorancin Shugaban kasa Muhammad Bazoum.