Daga Kamal Umar Kurna
Gwamnatin jihar Kano tace ta kaddamar da aikin tantance ma’aikatan hukumar kwashe shara da tsaftar muhalli ta jihar, ne domin gano bara gurbi da gano matsalolin wasu daga cikin ma’aikatan suke fuskanta domin inganta ayyukansu.
Kwamishinan Ma’aikatar Muhalli ta jihar Kano Honourable Nasiru Sule Garo ne ya bayyana hakan lokacin da yake kaddanar da aikin tantance ma’aikatan a hukumar kwashe shara da tsaftar muhalli ta jihar nan.

Garo yace duba da yadda koke suka yi yawa daga cikin ma’aikatan hukumar musamman kanana ma’aikatarsa, hakan yasa gwamnati taga dacewar tantance ma’aikatan tare da yin garanbawul domin samun cikakkiyar nasarar ayyukan Ma’aikatar.
Da dumi-dumi: Muhimman gabobi 5 na Jawabin Shugaban Tinubu
Da yake jawabi tun da farko tsohon shugaban hukumar kwashe shara ta jihar Kano Injiniya Abdullahi Shehu Wanda shine shugaban kwamitin tantance ma’aikatan, ya bukaci hadin kan ‘yan kwamitin nasa domin gudanar da aikin cikin nasara.
Daga karshe kwamishinan Ma’aikatar Muhallin ta jihar Honourable Nasiru Sule Garo yace kwamitin zai yi aikinsa cikin kwanaki 5 tare da Mika rahotonsa.