Daga Zainab Kabir Kundila
A daren wannan rana ta litinin Shugaban kasar Nigeria Bola Tinubu ya gabatar da jawabi ga al’ummar Kasar kan halin da tattalin arzikin Nigeria yake ciki.
Kadaura24 ta rawaito a cikin jawabin da shugaban kasar yayi ya tabo al’amura daban-daban musamman wadanda suka shafi tattalin arzikin kasa da Kuma manufofin sa akan tattalin arzikin har ma da batun cire tallafin mai fetur.

1 – Matun janye tallafin man fetur
Shugaban kasa Bola Tinubu yace ba shi da yadda zai yi dole ce tasa ya janye tallafin da gwamnatin tarayya ta ke baiwa man fetur, saboda yadda ya fuskanci wasu tsiraru ne suke amfana da tallafin wanda ya kamata al’ummar Nigeria baki dayansu ya kamata su mora.
Yace a cikin watanni biyu gwamnatinsa ta sami nasarar tara kudaden da yawansu ya kai sama da Naira tiriliyan guda , ya kuma baiwa al’ummar Nigeria tabbacin za’a yi amfani da kudaden ta yadda al’ummar Nigeria zasu amfana.
2 – Yadda ake baiwa wasu kudaden kasashen waje
Shugaba Tinubu ya kuma yi tsokaci akan yadda ake baiwa wasu shafaffu da mai kudaden kasashen waje wanda yake hakan ya taimaka matuka wajen durkusar da tattalin arzikin Nigeria.
“Wannan labarin yana bani takaici shi yasa muka ɗauki matakan dakatar da yadda ake baiwa wasu shafaffu da mai kudaden kasashen waje, mun dawo da tsarin yadda kowa zai amfana don gina tattalin arzikin kasar mu” . A cewar sa
Yajin aiki: Majalisar Dattawa za ta gana da gwamnatin tarayya da kungiyar ƙwadago
3 – Samar da Motocin Sufuri
Shugaban kasar yace saboda samar da sauƙi ga al’ummar Nigeria sakamakon cire tallafin man fetur, gwamnatin tarayya zata bada tallafin motoci ga gwamnatocin jihohi da kananan hukumomi don saukaka harkokin Sufuri a kasa.
Yace motocin zasu taimaka matuka wajen saukakawa al’ummar Nigeria, Inda jihohin zasu biya kudaden motocin cikin sauki da rangwame duk don saukakawa al’ummar Nigeria.
Gwamnatin Kano ta bayyana dalilin Sanya hoton Muhd Sanusi II a dakin taro na Coronation
4 – Tallafawa Kamfanonin guda 75
Shugaban Najeria Bola Ahmed Tinubu yace gwamnatin tarayya zata baiwa kamfanoni guda 70 tallafin Naira Biliyan 1 kowannesu don bunkasa aiyukansu da kuma samar da aiyukan yi ga al’ummar Nigeria.
Yace tallafin za’a bada shi ne bashi mai karancin ruwa, Inda masu kamfanonin zasu biya kaso 9 na kudin ruwan kuma zasu biya kudaden ne cikin watanni 60, yace an yi hakan ne don bunkasa aiyukan masana’antun da tattalin arzikin Nigeria .
5 – Tallafawa Kananan Yan Kasuwa
Shugaba Tinubu yace a kokarinsa na saukakawa al’ummar Nigeria gwamnatin tarayya zata bada tallafin Naira Miliyan 1 ga yan kasuwa masu kanana da matsakaitan masanan’antu don ingantawa da habbaka tattalin arzikin Nigeria.
Yace zasu kashe Naira Biliyan 125 wajen tallafawa kanana da matsakaitan masanan’antu, Inda za’a basu bashi da kuɗin rawa kadan domin baiwa yan kasuwar damar inganta aiyukansu kuma za’a fara bayar da tallafin ne daga watan Yuli na Shekarar 2023 zuwa watan Maris na Shekara ta 2024.
Ya kuma ya bayani akan kokarinsa na ganin ya karawa ma’aikatan gwamnati albashi kamar yadda kungiyar ƙwadago take bukatar, Inda yace karin zai zo nan ba da jimawa ba.
Shugaba Tinubu ya kuma bada tabbacin yana kokari wajen ganin an daidaita fara shin kayan abinchi a kasar, domin saukakawa al’umma. Yace za’a fito da hatsi akalla tan 200 domin rabawa ga mabukata a jihohin 36 na kasar nan.
A jawabin nasa Bola Tinubu ya tabbatar da cewa yana sane da halin matsin rayuwa da al’ummar Nigeria suke ciki, kuma yace yana yin duk mai yiyuwa wajen ganin ya fito da tsare-tsaren da zasu saukaka al’umma.
Ya kuma baiwa al’ummar Nigeria hakuri bisa halin da suka shiga sakamakon janye tallafin man fetur.