Daga Khadija Abdullahi Aliyu
A ranar Litinin ne majalisar dattawa ta umurci shugabanninta da su gana da gwamnatin tarayya da kuma kungiyar kwadago ta Najeriya domin dakile yajin aikin da kungiyar ke shirin yi a fadin kasar.
Idan dai za a iya tunawa kadaura24 ta rawaito cewa, kungiyar NLC ta bai wa gwamnatin tarayya wa’adi kan janye tallafin man fetur ko kuma ta fuskanci yajin aikin gama gari daga ranar Laraba 2 ga watan Agusta, 2023.

A halin yanzu kungiyar ta ƙwadago tana ta kokarin haɗa kan ƙungiyoyi don tabbatar da cewa yajin aikin ya yi nasara kamar yadda suke fata.
Kudurin majalisar ya biyo bayan wani kudiri mai taken: “Bukatar gaggawar dakile yajin aikin da kungiyar kwadago ta Najeriya ke shirin yi a fadin kasar saboda cire tallafin man fetur” wanda Sanata Sulaiman Kawu (NNPP-Kano ta Kudu) ya gabatar .
Gwamnatin Kano ta bayyana dalilin Sanya hoton Muhd Sanusi II a dakin taro na Coronation
Kawu Sumaila da yake gabatar da kuɗirin ya dage cewa yajin aikin zai yi mummunar illa ga tattalin arzikin kasar idan aka bari aka fara shi.
Sanatocin da suka goyi bayan kuɗirin sun haɗar da Isah Jibrin, Seriake Dickson, da Solomon Adeola .
Sun yi kira ga kungiyar NLC da ta janye shirin ta na tafiya yajin aikin da ta ke yi, ta kuma ba da dama ga ayyukan jin kai da gwamnatin tarayya ke shiryawa domin magance radadin da jama’a ke ciki.
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya yi kira ga kananan hukumomi da gwamnatocin jihohi da su hada kai don magance wahalhalun da jama’a ke ciki. Ba za mu iya ci gaba da amfani da kashi 98 cikin 100 na kudaden shiga don bada tallafin mai ba.