Kungiyar Tarayyar Turai ta EU ta dakatar da taimakon soji da take bai wa Nijar bayan kifar da gwamnatin ƙasar da sojoji suka yi.
Ana yi wa Mohamed Bazoum kallon babban abokin ƙasashen yamma, a ƙoƙarin da yake yi kakkaɓe ayyukan masu iƙirarin jihadi a yankin Sahel.
baya.

A ranar Juma’a ne shugaban dakarun da ke tsaron fadar shugaban ƙasa Janar Abdourahmane Tchiani ya ayyana kansa a matsayin sabon shugaban ƙasar.
Dangote ya Magantu kan rade-radin ya dauki yan India 11,000 aikin gina matatar mansa
A yayin wani jawabi da ya gabatar Janar Tchiani ya ce taɓarɓarewar tsaro da tattalin arziki da kuma cin hanci da rashawa ne suka sanya shi ƙwace mulkin ƙasar.
Matakin na zuwa jim-kaɗan bayan da Amurka ta sanar da matakin bai wa hamɓararren shugaban ƙasar goyon
To sai dai ƙasashen yamman na nuna fargaba game da ƙasashen da sabon shugaban ƙasar zai ƙulla ƙawance da su.
Duka makwabtan Nijar, Burkina Faso da Mali sun karkatar da ƙawancensu ga ƙasar Rasha tun bayan da aka yi juyin mulki a ƙasashen.
BBC Hausa ta rawaito she hugaban hukumar kula da al’amuran ƙasashen waje na ƙungiyar EU Josep Borrell ya bi sahun Amurka da Faransa wajen ƙin amincewa da sabbin juyin mulkin, yayin da ya ce taimakon soji da na agaji da ƙungiyar ke bai wa Nijar ya tsaya ba tare da ɓata lokaci ba.
Haka kuma ita ma ƙungiyar haɗin kan Afirka ta AU ta yi kira ga sojojin Nijar da su koma sansanoninsu cikin kwanaki 15.