Dangote ya Magantu kan rade-radin ya dauki yan India 11,000 aikin gina matatar mansa

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 

Hukumar kula da matatar man Dangote ta karyata wani rahoto da aka wallafa a shafukan sada zumunci wanda ke cewa kamfanin ya dauki kwararrun ma’aikata 11,000 daga kasar Indiya Maimakon ya dauki matasa daga Najeriya da wasu kasashen Afirka.

 

A martanin da ya mayar, babban jami’in hulda da jama’a na kamfanin, Anthony Chiejina, ya ce an rubuta rahoton ne da mugun nufi domin bai nuna adadin kwararrun ‘yan Najeriya da ke aiki a matatar ba.

Yanzu-Yanzu: Sojojin Nijar sun Bayyana Sabon Shugaban Kasar

Ya ce, girman aikin na bukatar kwararrun ma’aikata na musamman daga ko’ina a duniya, kuma sama da ‘yan Nijeriya 30,000 na daga cikin kwararrun ma’aikata da aka ɗauka aikin tun lokacin da aka fara aikin gina matatar, an kuma ɗauki Indiyawa 6,400 aiki yayin da aka dauki yan china kimanin 3,250 aiki a matatar man ta Dangote.

 

Ya kuma ce ’yan Najeriya da ke aiki a matatar suna nuna kwarewa sosai saboda irin hikima da basirar da Allah ya basu.

Talla

Ya shawarci jama’a da su yi watsi da irin wadancan rahotanni na bata-gari marasa kishi, maimakon haka su mai da hankali kan alfanun da aikin zai iya haifarwa ga tattalin arzikin kasa baki daya da walwalar ‘yan Nijeriya ganin yadda rukunin Dangote ke ci gaba da kasancewa kan gaba wajen samar da ayyukan yi ga matasa a Nigeria.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Wata sabuwa: Sanata Barau Jibrin ya gana da Baffa Bichi da Muhd Diggol

Tsohon sakataren gwamnatin Jihar Kano Dakta Abdullahi Baffa Bichi...

Rikicin Masarautar Kano: Kotu ta Sake Sabon Hukunci

A wani sabon yanayi na rikicin Masarautar Kano, Kotun...

Gidauniyar Aliko Dangote za ta rabawa ‘yan Najeriya miliyan daya shinkafa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Gidauniyar Aliko Dangote ta raba buhunan...

Rufe Makarantu da azumi: Ministan Ilimi ba ta da ilimin harkokin mulki – Jafar Sani Bello

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Tsohon dan takarar gwamnan jihar Kano...