A shirye muke don huldar Kasuwanci da masu son zuba jari a Nigeria- Tinubu

Date:

Daga Aliyu Nasir Zangon aya

 

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ce Najeriya a shirye take don huldar kasuwanci, sannan kuma ta samar da kyakyawan yanayi ga masu son zuba jari.

 

Shugaban ya bayyana haka ne a ranar Alhamis a birnin Paris na kasar Faransa, yayin da yake karbar bakuncin shugaban kwamitin gudanarwa na bankin shigo da kayayyaki na Afirka (Afrexim), Farfesa Benedict Oramah, da shugaban bankin Turai da raya kasa (EBRD), Odile Renaud. -Basso, yayin wani taro na daban, yayin da yake halartar taron koli na Sabuwar Yarjejeniyar Kudade ta Duniya.

Binciken bidiyon Dala: Ganduje ya mayarwa Muhuyi Magaji Martani

“Muna shirye don kasuwanci, kuma muna maraba da masu zuba jari,” in ji shi, ya kara da cewa sauye-sauyen da ake ci gaba da gudanarwa a Nigeria, da suka hadar da farawa da cire tallafin man fetur da daidaita farashin canjin kudaden kasashen waje, Inda yace hakan zai taimaka wajen samun ingantaccen tattalin arziki wanda ke jawo hankalin masu zuba jari kai tsaye na kasashen waje (FDI).

Danbilki Kwamanda ya Koka da matakin da yace gwamnatin Kano ta ɗauka akansa

Ya bukaci masu zuba jari da su yi amfani da damar da Nigeria ta basu wajen zuba jarinsu don yin harkokin kasuwanci a Kasar.

Tallah

Shugaba Tinubu, a wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Dele Alake, ya fitar, ya tabbatar wa tawagar shugabannin bankin Afrexim Bank karkashin jagorancin Dr Oramah cewa, gwamnatin tarayyar Nigeria za ta ci gaba da bunkasa tattalin arzikin kasar, tare da fito da manufofin da zasu tallafawa masu zuba jari da kuma jawo hankalin su don zuba jari ta a fannonin daban-daban a Nigeria.

Shugaba Tinubu ya shaida wa tawagar, Nigeria tana da tarin jama’a, wanda tun da farko ya zayyana hanyoyin da za a bi wajen bunkasa tattalin arzikin kasar, kamar kayayyakin more rayuwa, kiwon lafiya, makamashi da kuma noma.

Shugaban bankin na AfreximBank ya yabawa shugaba Tinubu kan matakin da ya dauka na cire tallafin man fetur da kuma daidaita farashin canji, inda ya baiwa shugaban Najeriyar tabbacin samun cikakken goyon bayan hukumar kudi da raya kasa kan sauye-sauyen da ake yi a kasar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Wata sabuwa: Sanata Barau Jibrin ya gana da Baffa Bichi da Muhd Diggol

Tsohon sakataren gwamnatin Jihar Kano Dakta Abdullahi Baffa Bichi...

Rikicin Masarautar Kano: Kotu ta Sake Sabon Hukunci

A wani sabon yanayi na rikicin Masarautar Kano, Kotun...

Gidauniyar Aliko Dangote za ta rabawa ‘yan Najeriya miliyan daya shinkafa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Gidauniyar Aliko Dangote ta raba buhunan...

Rufe Makarantu da azumi: Ministan Ilimi ba ta da ilimin harkokin mulki – Jafar Sani Bello

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Tsohon dan takarar gwamnan jihar Kano...