Daga Rahama Umar Kwaru
A ranar Alhamis ne wata kotun shari’ar Musulunci a jihar Kano ta bayar da umarnin tsare wani matashi dan shekara 25, Aliyu Sa’ad, wanda ya amsa laifin kiran abokinsa dan luwadi, a gidan gyaran hali.
Alkalin kotun, Malam Umar Lawal-Abubakar, ya bayar da umarnin ne biyo bayan amsa laifin da Sa’ad ya shigar.
Za mu samar da sabbin wuraren kasuwanci a Kano don rage cunkoso a birnin jihar – Abba Gida-gida
Lawal-Abubakar ya dage ci gaba da sauraron karar har zuwa ranar 3 ga watan Yuli domin ci gaba da shari’ar.
Tun da farko, Lauyan masu shigar da kara, Insp Abdullahi Wada, ya shaida wa kotun cewa wanda ake kara ya aikata laifin ne a ranar Litinin da misalin karfe 8 na dare.

Wada ya kuma ce wanda ake kara ya kira wanda yake kara, Malam Ahmed Khamis-Ahmed da sunan da bai dace ba bayan wata hatsaniya da sukai.
Mai gabatar da kara ya ce laifin ya ci karo da tanadin sashe na 188 na shari’ar Musulunci ta jihar Kano.