Daga Maryam Ibrahim Muhammad
Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, a yau Laraba, ta ba da umarnin mayar da Mahdi Ali Gusau a matsayin mataimakin gwamnan jihar Zamfara, biyo bayan tsige shi da majalisar dokokin jihar ta yi a ranar 23 ga watan Fabrairun 2022, duk kuwa da umarnin kotu na hani da cire shin.
Sai dai kuma Mai shari’a Inyang Ekwo, a hukuncin da ya yanke, ya kuma rushe duk wani mataki da majalisar ta dauka, da tsohon Gwamna Bello Matawalle da alkalin alkalan jihar na tsige Gusau a lokacin da ake shigar da kara a gaban kotu.
Za’a karawa Tinubu da sauran shugabanni a Nigeria Albashi
Mai shari’a Ekwo, wanda ya ce abin da kakakin majalisar na wancan lokacin, tsohon gwamna, babban alkalin alkalai da sauran su suka yi, ya zama maras amfani yanzu, ya bayyana shi a matsayin “ rusashshe kuma ba shi da wani tasiri.”

Ekwo ya ce shi bai ga dalilî da hujjoji na shari’a da za su sanya a tsige mataimakin gwamnan ba.
Sai dai kuma Daily Nigerian Hausa ta fahimci cewa duk da kotu ta mayar da shi, Mahdi ba shi da ikon zama Mataimakin Gwamna a halin yanzu tun da ba da shi a ka yi zaɓen 2023 ba.