Za’a karawa Tinubu da sauran shugabanni a Nigeria Albashi

Date:

Hukumar tattarawa da raba kuɗaɗen shiga a Najeriya ta amince da ƙudurin ƙarin albashin zaɓaɓɓun ‘yan siyasa ciki har da shugaban ƙasa da mataimakinsa.

 

Ƙudurin zai kuma shafi gwamnoni da mataimakansu da ‘yan majalisa da alƙalai da sauran masu riƙe da muƙaman gwamnati.

Danbilki Kwamanda ya Koka da matakin da yace gwamnatin Kano ta ɗauka akansa

Ta ce ƙarin wanda aka yi a kan tsagwaron albashi (ban da alawus-alawus) ya kai kashi 114, abin da ke nufin shugaban ƙasa zai iya karɓar albashin da ya kusan kai naira miliyan biyu duk wata.

 

Shugaban hukumar (RMAFC) Muhammadu Shehu ya faɗa wa BBC cewa sun yi nazari bisa la’akari da halin da ake ciki a ƙasa, kafin yin ƙarin albashin.

Da dumi-dumi: Shekarau ya Magantu kan gayyatar da Majalisar Dinkin duniya ta yi masa

Sai dai a cewarsa, matakin ƙuduri ne kawai don kuwa sai an gabatar wa Majalisar Tarayya don amincewa kafin ya zama doka.

Tallah

Haka zalika ƙarin zai shafi ministoci da kwamishinoni da mataimaka na musamman kamar yadda sashe na 84 da sashe na 124 na tsarin mulkin Najeriya ya tanada.

 

A cewar hukumar, karon ƙarshe da aka yi wa zaɓaɓɓun ‘yan siyasar ƙarin albashi a Najeriya, shi ne shekara ta 2007.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Wata sabuwa: Sanata Barau Jibrin ya gana da Baffa Bichi da Muhd Diggol

Tsohon sakataren gwamnatin Jihar Kano Dakta Abdullahi Baffa Bichi...

Rikicin Masarautar Kano: Kotu ta Sake Sabon Hukunci

A wani sabon yanayi na rikicin Masarautar Kano, Kotun...

Gidauniyar Aliko Dangote za ta rabawa ‘yan Najeriya miliyan daya shinkafa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Gidauniyar Aliko Dangote ta raba buhunan...

Rufe Makarantu da azumi: Ministan Ilimi ba ta da ilimin harkokin mulki – Jafar Sani Bello

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Tsohon dan takarar gwamnan jihar Kano...