Danbilki Kwamanda ya Koka da matakin da yace gwamnatin Kano ta ɗauka akansa

Date:

Daga Aisha Aliyu Umar

 

Shahararren Mai adawa da gwamnatin jihar kano ta Abba Gida-gida da Kwankwasiyya a Alhaji Abdulmajid Danbilki Kwamanda ya zargi gwamnatin da hana shi zuwa aikin Hajjin bana .

 

” Nasan adawar da nake da gwamnatin jihar kano ce tasa aka hanani visa domin tafiya hajjin bana, saboda duk yarana da na biya mana naira Miliyan 15 a Abuja su sun samu sai ni saboda Ina adawa da su, to adawa yanzu na fara ta”. Danbilki

Da dumi-dumi: Abba Gida-gida ya nada mukaddashin mai magana da yawunsa

Kwamanda yayin zargin ne a wata hira da yayi a shafinsa na Facebook domin sanar da duniya halin da ya shiga.

 

Yace Bayan samun labarin babu sunansa cikin yan karamar hukumar Bunkure da zasu tafi kasa mai tsarkin, yace je har sansanin alhazan Kano, Inda ya iske Darakta janar na hukumar jin dadin alhazai ta jihar kano, domin jin matsalar da ta hana sunanshi fitowa cikin masu tafiya saudiyya.

Tallah

” Bayan na tambaye shi , sai yace da ni wai gwamnatin baya ce ta ja min, bayan kuma ni a Abuja na biya kudina, kuma tuni aka bani jaka da ID card na tafiya amma wai yace min matsalata gwamnatin baya ce ta jawo min, daga ƙarshe dai kawai na fahimci sun hana ni zuwa makka ne inyi ibada, kawai don ina adawa da su”. A cewar Kwamanda

Da dumi-dumi: Shekarau ya Magantu kan gayyatar da Majalisar Dinkin duniya ta yi masa

Danbilki Kwamanda dai ya yi kaurin suna wajen nuna adawa da gwamnatin kwankwasiyya ta Engr. Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP.

Mun tuntubi Darakta janar na hukumar jin dadin alhazai ta jihar kano Alhaji Lamin Rabi’u don Jin ta bakinsu kan zargin da Danbilki Kwamanda yayi akan su, Amma bai daga wayarmu har lokacin haɗa wannan rahoto.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Wata sabuwa: Sanata Barau Jibrin ya gana da Baffa Bichi da Muhd Diggol

Tsohon sakataren gwamnatin Jihar Kano Dakta Abdullahi Baffa Bichi...

Rikicin Masarautar Kano: Kotu ta Sake Sabon Hukunci

A wani sabon yanayi na rikicin Masarautar Kano, Kotun...

Gidauniyar Aliko Dangote za ta rabawa ‘yan Najeriya miliyan daya shinkafa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Gidauniyar Aliko Dangote ta raba buhunan...

Rufe Makarantu da azumi: Ministan Ilimi ba ta da ilimin harkokin mulki – Jafar Sani Bello

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Tsohon dan takarar gwamnan jihar Kano...