Daga Isa Ahmad Getso
Gwamnan Jihar Kano Engr. Abba Kabir Yusuf ya amince da nadin Malam Hisham Habib a matsayin mukaddashin Babban Sakataren Yada Labaransa kafin jiran dawowar mai magana da yawunsa Sanusi Bature Dawakin Tofa wanda zai bar Najeriya ya jagoranci tawagar yada labaran Kano zuwa aikin Hajjin bana.
Hisham, kwararre ne kan harkokin yada labarai wanda ya shafe sama da shekaru ashirin yana aikin yada labarai a kwanan baya ya taba rike mukamin daraktan yada labaran kwamitin yakin zaben jam’iyyar NNPP a zaben 2023 a jihar Kano.
Babu Kwamishina da za a rantsar ba tare da bayyana kadarorinsa ba – Abba Gida-gida
Hakan zai na kunshe ne cikin wata sanarwa da babban Sakataren yada labaran gwamnan Sanusi Bature Dawakin Tofa ya aikowa kadaura24.
Ana sa ran zai karbi sabon mukamin na rikon kwarya nan take, gwamnan ya bukaci dukkan masu ruwa da tsaki a harkokin yada labarai da su ba shi cikakken goyon baya da hadin kai kamar yadda ya bai wa Bature Dawakin Tofa.