Ku baiwa Gwamnatoci hadin Kai su Kawo Karshen Yan ta’adda – Alh Shehu Ishiye

Date:

 

Daga Sani Haruna

Shugaban kwamitin amintattu, na Kungiyar cigaban Garin Dutsinma Dake jihar Katsina DDF, Alhaji Shehu Ishiye ya yi kira ga Yan Najeriya dasu tallafawa gwamnati tarayya dana Jihohi a kokarinsu na kawo karshen yan bindiga, da Masu garkuwa da Mutane da sauran Masu aikata munanan laifuka a kasar nan.

Ya bayyana hakan ne a wajen taron shekara-shekara na kungiyar wanda aka gudanar a karamar hukumar Dutsinma ta jihar Katsina.

Alhaji Shehu Ishiye ya ce za a iya samun hadin kai da zaman lafiya a kasar nan ne ta hanyar jajircewar kowa da kowa musamman wajen yaki da rashin tsaro da sauran abubuwan da ke haifar da koma Bayan ci gaban tattalin arzikin kasa.

A yayin taron, an kuma zabi sabbin mambobin kungiyar wadanda za su ci gaba da tafiyar da harkokin kungiyar har na tsawon shekaru biyu.

Wadanda aka zaba sun hada da Dr Sabiu Liyadi a matsayin Shugaba, Aliyu Ibrahim a matsayin Mataimakin Shugaba, Maikaita Abdullahi a matsayin Sakatare, Bishir Ibrahim Mataimakin Sakatare, Sakataren Kudi Hamza Abba Kasim, Ma’aji Ahamad Saad, Odita Adullahi Bature, Sakataren Walwala, Kabir Musa Yari, Sakataren yada labarai I Bishir Mamman Tanbu, da Sakataren Yada Labarai II Kabir Ibrahim Sada.

A jawabinsa na godiya a madadin sabbin shuwagabannin, Shugaban kungiyar Dakta Sabiu Liyadi ya yabawa dukkan mambobin saboda dattako, kauna da jajircewa da aka nuna yayin gudanar da zaben da kuma kwamitin zaben bisa ga namijin kokarinsu da juriyar da suka nuna don ganin anyi zabe Cikini nasara.

Ya yi alkawarin haɗa Kai da sauran masu ruwa da tsaki domin ciyar da Kungiyar gaba, ya Kuma ce Zai haɗa Kai da karamar hukumar Datsinma da jihar Katsina baki daya, tare Kuma da kara inganta alakar Kungiyar da daidaikun al’umma kuma ya tabbatar da gudanar da Shugabanci na Gari tare da barin kifarsa a bude don karbar shawarwarin da zasu taimaka wajen inganta harkokin Kungiyar.

An kirkiro Kungiyar Dutsinma Development Forum ne da nufin inganta rayuwar mazauna yankin da ma jihar baki daya ta fuskar tattalin arziki, zamantakewa da kuma halaye na gari

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yanzu-yanzu: An zabi sabon shugaban jami’ar Bayero BUK

Daga Rahama Umar kwaru   Farfesa Haruna Musa ya zama sabon...

An sake sauya lokacin jana’izzar Aminu Ɗantata – Gwamnatin Nigeria

Gwamnatin tarayyar Nigeria ta ce Hukumomi a Kasar Saudiyyar...

Fadan daba: ku fito ku Kare Kan ku da iyayenku – Gwamnatin Kano ga matasa

Ku tashi ku Kare kanku da iyayen Gwamnatin jihar kano...