Daga Abubakar Lawan Bichi
Shugaban Kasa Bola Ahmad Tunubu ya Amince da nadin masu bashi shawara guda takwas.
Hakan na kunshe a wata sanadar da daratar yada labarai na fadar Shugaban Kasa Abiodun Oladunjoye ya fitar.
Wanda aka nada sun hada :
1. Mr. Dele Alake Mai bawa shugaban Kasa Shawara aka Ayyuka na musamman, Sadawa da kuma tsare tsare.
2. Mr Yau Darazo mai bawa shugaban Kasa Shawara akan harkokin Siyasa.
3. Mr Wale Edun mai bawa shugaban Kasa Shawara aka harkokin tsare tsare kudin.
Yanzu-Yanzu: Ginin Daula Otal ya fadawa wasu matasa masu dibar ganima
4. Mrs Olu Verheijen Mai bawa shugaban Kasa Shawara aka harkokin makamashi.
5. Mr Zachaeus Adedeji mai bawa shugaban Kasa Shawara aka harkokin Kudaden shiga.
Gwamnatin Kano za ta rushe Masarautun Gaya, Rano, Bichi da Karaye da Kuma dawo da Sarki Sunusi
6. Mallam Nuhu Ribadu mai bawa shugaban Kasa Shawara aka harkokin Tsaro.
7. Mr John Ugochukwu mai bawa shugaban Kasa Shawara aka harkokin Masana’antu da kuma zuba Jari.
8. Dr (Mrs.) Salma Ibrahim Anas Mai bawa shugaban Kasa Shawara aka harka Lafiya
Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito cewa majalisar tarayyar ta kasa ta amincewa Shugaban kasa Bola Tinubu ya nada masu bashi shawara na musamman har guda 20.