Daga Kamal Yahaya Zakaria
Gwamnatin jihar kano ta bayyana cewa zata mika sunayen Kwamishinoni ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa kamar yadda doka ta tanadar.
“Ana sa ran a mako mai zuwa za a aika da jerin sunayen sunayen kwamishinonin da gwamna zai yi aiki da su a matsayin yan majalisar zartarwa gwamnatin sa ga majalisar dokokin jihar kano domin tantancewa”.
Gwamnatin Kano za ta rushe Masarautun Gaya, Rano, Bichi da Karaye da Kuma dawo da Sarki Sunusi
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da babban Sakataren yada labaran gwamna Sanusi Bature Dawakin Tofa ya aikowa kadaura24.
Hotuna: yadda Aka rushe shatale-talen dake Kofar gidan gwamnatin kano
Sanarwar ta musanta labarin da ke cewa gwamnatin ta mikawa majalisar dokokin jihar kano bukatar sake duba dokar Masarautu domin rushe sabbin da kuma dawo da tsohon Sarkin Kano Muhammad Sanusi II.
“Sabanin jita-jitar da ake yadawa a shafukan sada zumunta, gwamnatin jihar Kano ba ta dau wani mataki kan sabbin masarautun kamar yadda ake hasashe”. A cewar Sanusi Bature
Za’ a rika yiwa al’ummar jihar kano bayani akan duk wani da gwamnatin Kano zata yi musamman abun da ya shafi tsakanin bangaren zartaswa da na ‘yan majalisar dokoki domin yin komai a bude.
Gwamna ya mika bukatar nada masu ba da shawara na musamman guda 20 wanda majalisar dokokin jihar ta amince da su a zamanta na yau.