Gwamnatin Kano za ta rushe Masarautun Gaya, Rano, Bichi da Karaye da Kuma dawo da Sarki Sunusi

Date:

Daga Nura Garba Jibril

 

Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf na shirin aika kudirin gyara dokar masarautar Kano ga majalisar dokokin jihar .

 

A Kudirin dokar zai nemi soke karin masarautun guda hudu da suka hada da Bichi, Gaya, Rano da kuma Karaye masu daraja ta daya.

 

Wannan dai shi ne zai zama aiki na farko a hukumance da majalisar dokokin jihar Kano zata yi wadda aka kaddamar a ranar 13 ga watan Yuni kuma ta zabi Jibrin Falgore na karamar hukumar Rogo a matsayin shugaban majalisar.

Yanzu-Yanzu: Gwamnatin Kano ta bayyana dalilin da yasa ta rushe shatale-talen gidan gwamnati

Idan dai ba a manta ba a shekarar 2019 ne tsohon gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya aika da wata doka ga majalisar dokokin jihar domin amincewa da sabuwar dokar.

 

An ragewa Sarkin Kano na lokacin, Muhammadu Sunusi karfin ikon sakamakon bar masa kananan hukumomin goma kacal daga cikin 44 da yake rike da su.

Hotuna: yadda Aka rushe shatale-talen dake Kofar gidan gwamnatin kano

Bisa ga kudirin dokar, masarautar Kano ta kunshi kananan hukumomin Kano Municipal, Tarauni, Dala, Nassarawa da Fagge. Sauran kananan hukumomin da ke masarautar Kano sun hada da Gwale, Kumbotso, Ungogo, Dawakin Kudu da Minijibir.

Kananan hukumomin Karaye, Rogo, Gwarzo, Kabo, RiminGado, Madobi da Garun Malam, suna karkashin masarautar Karaye a cikin kudirin dokar.

Masarautar Bichi ta kunshi kananan hukumomin Bichi, Bagwai, Shanono, Tsanyawa, Kunchi, Makoda, Danbatta, Dawakin Tofa da Tofa.

‘Yan majalisar sun sanya sunayen kananan hukumomin Rano, Bunkure, Kibiya, Takai, Sumaila, Kura, Doguwa, Tudun Wada, Kiru da Bebeji a karkashin masarautar Rano.

Masarautar Gaya tana da kananan hukumomin Ajingi, Albasu, Wudil, Garko, Warawa, Gezawa and Gabasawa and Gaya .

Ma’anar samar da karin masarautu shi ne, za a rage karfin ikon Sarkin Kano Malam Muhammad Sanusi ll.

Majiyar Kadaura24 ta POLITICS DIGEST ta rawaito cewa za a gabatar da kudirin a zauren majalisar ranar Alhamis, wanda shugaban masu rinjaye Lawan Hussaini na mazabar Dala ne zai karanta .

Da aka tuntubi dan majalisar kan lamarin, dan majalisar ya musanta labarin da ke gudana cewa babu wani abu mai kama da wannan.

Ya shaida wa wakilin politics digest cewa zai yi ganawa da manema labarai a ranar Alhamis akan lamarin.

Tun farko jagoran tafiyar Kwankwasiyya Rabiu Kwankwaso yayi Allah wadai da kafa sabbin masarautun a wasu jawabai daban daban da ya rika yi kafin zabe.

Daga cikin ajandar sabuwar gwamnati akwai rusa wasu gine-gine da aka gina a karkashin gwamnatin Ganduje da kuma sauya dokar masarautar Kano.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sake jaddada matsayinsa na dawo wa jihar kano Kano darajar ta.

A cewarsa, al’ummar Kano ne suka zabe shi a kan haka kuma zai yi duk mai yiwuwa don cika alkawarin da ya dauka kafin zabe.

“Idan aka amince da sabuwar dokar, jihar za ta kasance da sarki mai daraja daya kacal.

Wata majiya da ta so a sakaya sunanta ta shaida wa Majiyar ta mu cewa, mai yiwuwa a tsige Sarkin Kano na yanzu Aminu Ado Bayero ne domin share wa dan uwansa Muhammadu Sunusi hanyar komawa kan karagar kakanninsa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Wata sabuwa: Sanata Barau Jibrin ya gana da Baffa Bichi da Muhd Diggol

Tsohon sakataren gwamnatin Jihar Kano Dakta Abdullahi Baffa Bichi...

Rikicin Masarautar Kano: Kotu ta Sake Sabon Hukunci

A wani sabon yanayi na rikicin Masarautar Kano, Kotun...

Gidauniyar Aliko Dangote za ta rabawa ‘yan Najeriya miliyan daya shinkafa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Gidauniyar Aliko Dangote ta raba buhunan...

Rufe Makarantu da azumi: Ministan Ilimi ba ta da ilimin harkokin mulki – Jafar Sani Bello

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Tsohon dan takarar gwamnan jihar Kano...