Daga Safiyanu Dantala Jobawa
Fiye da masallata miliyan biyu ne suka halarci masallacin harami da ke Makka da kuma masallacin Annabi da ke Madina domin halartar sallolin tarawi a daren ranar 27 ga watan Ramadan don neman dacewa da daren Laylatul Qadari.
Jaridar Saudi gazzet ta ruwaito shugaban masallatan biyu masu alfarma Sheikh Abdul Rahman Al-Sudais ne ya bayyana haka a lokacin da yake yaba wa tsare-tsaren da masalallatan suka yi domin bai wa masallata damar gudanar da ibadunsu cikin kwanciyar hanakali
Da dumi-dumi : INEC ta bayyana Matsayarta kan Zaben Gwamnan Jihar Adamawa
Ya ce kusan masu ibada miliyan ɗaya da rabi ne suka halarci sallar dare a masallacin harami da ke Makka, wanda Sheikh Abdul Rahman Al-Sudais ɗin ya jagoranta.
Akan samu tururuwar masu sallar dare a dararen ranakun mara musamman dare 27 domin neman dacewa da daren Laylatul Qadr, saboda tarin alkairan da ke tattare da daren.
Hukumomin Saudiyya sun samar da wadatattun jami’an tsaro waɗanda suka taimaka wa masu ibada wajen gudanar da ibadunsu cikin tsari, da kwanciyar hankali duk kuwa da irin cunkoson jama’a da aka samu a wajen ibadar.