Daga Rabi’u Usman
Kimanin iyayen marayu Sama da 200 ne suka Amfana da tallafin kayan Sallah daga Shahararriyar Jarumar Masana’antar Kannywood Saratu Gidado wadda akafi sani da (Daso).
A ranar litinin ne dai Saratu Gidado ta tara iyayen marayu mata domin basu tallafin kayan sallah Atamfofi kowacce turmi 1 domin sanya farin ciki a zukatan su da kuma zamar dasu tamkar Mazajen su ko iyayen su suna Raye.
Ƙungiyar tallafawa marayun Karaye ta baiwa iyayen marayun 1500 tallafin kayan abinchi
Da take ganawa da wakilin Kadaura24, Saratu Gidado wadda akafi sani da (Daso) ta bayyana dalilin da yasa tayi wannan gagarumin aikin Alkhairin, inda tace tayi wannan rabon ne da Kudin Kamfanin ta na Daso Entertainment, wannan karon bata samu tallafi daga Hannun jama’a ba, kawai dai tayi amfani da Kudin da take samu a kamfanin ta ne.
” Dama Ina da burin gani Ina tallafawa masu karamin karfi kamar marayu da Iyayen su, shi yasa da ban sami tallafin al’umma ba sai na yi amfani da dan abun da Allah ya hore min don sanya farin ciki a zukatan wadannan bayin Allah”. Inji Daso
Tayi kira ga masu rike da madafun Iko da masu hannu da shuni da su dinga taimakawa marasa karfi ta bangaren kayan Abinci da kayan sakawa domin sanya farin ciki a zukatan su.
Wasu daga cikin mata iyayen Marayun da suka amfana da tallafin kayan Sallah daga wajen Daso, sun nuna Farin cikin su da kuma yin Godiya ga Saratu Gidado wadda ta taimaka musu da kayan sallah, musamman ta inda suka ce sun jima basu samu wanda yayi musu abin Alkhairin da Daso tayi Musu ba