Daga Halima Musa Sabaru
A ranar Juma’ar nan ne daliban nan mata guda biyu na jami’ar tarayya ta Gusau da aka sace a masaukinsu na haya dake kauyen Sabon Gida da ke karamar hukumar Bungudu sun samu ‘yanci a yau Juma’a.
Kungiyar dalibai ta jihar Zamfara (ZAMSSA) reshen jami’ar tarayya ta Gusau ce ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta rabawa manema labarai mai dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na kungiyar, Kwamared Umar Abubakar .
Ko da yake ba a bayyana ko an biya kudin fansa ko ba’a biya ba kafin a sako daliban Sashen Microbiology na jami’ar.
“Daliban mata biyun da aka sace na Sashen Microbiology na jami’ar sun koma cikin yan uwansu da sanyin safiyar ranar Juma’a 14 ga Afrilu, 2023 cikin koshin lafiya bayan kwanaki 12 a hannun yan ta’addan.” a cewar sanarwar