Kotu ta aike da wani matashi gidan Yari bisa zargin satar akwatin zaɓe a Kano

Date:

Daga Rahama Umar Kwaru

 

Kotun Majistre mai lamba 14, karkashin jagorancin alkali Mustapha Sa’ad Datti, ta aike da wani matashi zuwa kurkuku bisa zargin sa da kwace akwatin zaɓe, takardun dangwala kuri’a da kuma inkin dangwala kuri’a .

 

Lauya mai gabatar da kara, Barista Hajara Ado Saleh a jiya Juma’a ta shaidawa kotun cewa, matashin Ibrahim Jibrin Birged, ya shiga cikin makarantar firamare ta Gama, ƙaramar hukumar Nassarawa, tare da kwace akwatin zaɓen da sauran kayan zaɓe.

 

Sai dai kuma ya musanta tuhume-tuhumen da aka yi masa.

 

Alƙalin ya ɗage sauraron shari’ar zuwa 8 ga watan Maris, ya kuma bada umarnin a ci gaba da tsare matashin a gidan yari.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bai dace ɗalibai su rika murnar kammala karatu ta hanyoyin da ba su dace ba – Mal Ibrahim Khalil

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa ‎ ‎ ‎Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano...

Budaddiyar Wasika ga Gwamnan Kano kan wanda zai maye gurbin Muhuyi Magaji R/gado daga Kungiyar Lauyoyi yan Kano

Zuwa ga Mai Girma Alhaji Abba Kabir Yusuf Gwamnan Jihar Kano Gidan...

Dan majalisa Bichi ya sake biyan kuɗin makarantar dalibai 121 masu karatun digiri na biyu da na digirin digirgir

Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Mazabar Bichi a Majalisar...