Da kowanne jagora zai yi halin Abba Ganduje, da talakawa sun more –  Kabiru Inuwa Hayinhago

Date:

Daga Rahama Umar Kwaru

An bayyana Dan takarar majalisar Tarayya na yankin Dawakin Tofa Tofa da Rimingado a jam’iyyar APC, Eng. Umar Abba Ganduje, a matsayin Mai kaunar al’umma da kishin su.
 Mai ba gwamna Shawara kan manufofin gwamnati Kabiru Inuwa Hayinhago, ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa ta bangajiya da aikewa manema labarai, don nuna jin dadinsa bisa ziyarar ta’aziya da ya kai na dan uwansa, a garin Hayinhago da ke karamar hukumar Dawakin Tofa, a Ranar Juma’ar da ta gabata.
Talla
Talla daukar nauyi Suraj Umar Wudil
Kabiru Hayinhago, ya ce Abba Ganduje, ya nuna a fili mutum ne mai kaunar mutane, duba da yadda ya ke shiga lungu da sako na kananan hukumomin Dawakin Tofa, Rimingado da Tofa, don  gaisuwa da jajantawa al’umma bisa abubuwan da suka same su Mai dadi ko akasin haka.
” Ya zama wajibi mu godewa Allah da ya ba mu Abba Ganduje, hakika da sauran shugabanni za su yi ko yi da shi da an yi dace, duba da yadda ya ke shiga lungu da sako domin gaisuwa jaje ga mutane abin da an rasa a baya Shekaru Sha shida. Har wayau, Ina Kara Godiya Kan gaisuwar Dan uwa na da ya kawo” a cewar Hayinhago
.
Mashawarcin gwamnan, ya yi fatan al’ummar kananan hukumomin Dawakin Tofa Rimingado da Tofa zasu fito a ranar 25 ga watan fabarairun nan domin zabar Abba Ganduje, don ya wakilci al’ummar wakilci irin wanda ba a taba yi musu ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rasuwar Aminu Dantata: Duniyar Kasuwanci ta yi Babban Rashi – Shugaban Kamfanonin Gerawa

Shugaban rukunonin Gerawa group of Companies Dr. Ibrahim Muhammad...

Da dumi-dumi: Wasu kungiyoyin APC a Kano sun fara kiraye-kirayen Abdullahi Abbas ya sauka daga shugaban jam’iyyar

Daga Hafsat Abdullahi Muhammad Kungiyoyin jam'iyyar APC da suka hadar...

Bayan Amincewar Kasar Saudia , an Sanya Ranar Binne Aminu Dantata a Madina

Babban sakataren marigayi Alhaji Aminu Dantata, Mustapha Abdullahi Junaid...

Rashin Alhaji Aminu Dantata Babban Rashi ne ga harkokin kasuwanci a Duniya – Salbas

Daga Khadija Abdullahi Aliyu Babban kamfani a masana'antar mai a...