Wani Malamin addinin musulunci a jihar Kano, Sheikh Muhammad Dauda Lokon Makera, ya yi kira ga kungiyoyin addinai da mahukunta, da su ta shi tsaye domin dakile wani yunkuri da wata kungiyar ‘yan Luwadi, Madugo da canja jinsi a Najeriya wato (LGBT) take yi na ganin an zabi mutanen su a dukkanin matakai a kasar nan.
Kadaura24 ta rawaito Sheikh Dauda Lokon Makera, ya yi wannan kira ne lokacin da yake zantawa da manema labarai a kano.

Ya ce binciken da wani kwararren mai bincike Dr. Kwame lbrahim na cibiyar bincike ta African Research Institute ya gudanar ya gano cewa yanzu haka kungiyar bata garin ta sami nasarar dasa yan takarar su a jihohin Kano, Legas, Fatakwal, Ibadan, Imo, Maiduguri da birmin tarayya Abuja.

Malam Dauda yace akwai bukatar al’umma su lura da irin wadancan yan takara don gudun basu damar aiwatar da dokar halasta auren jinsi a Nigeria.
- ” A bayan kungiyar sun yi kokarin ganin an halasta auren jinsi a kasar nan, yan majalisu sukai fatali da kudirin da Wani dan majalisa gabatar, hakan tasa a yanzu sukai wannan dabarar ta dasa mutanen su a dukkanin jam’iyyar a takarar dan majalisar tarayya da kuma sanatoci don su sami rinjaye a majalisun, Saboda yi nasarar aiwatar da waccan mummunar Akida tasu”. A cewa binciken
Malam Dauda ya ce wajibi ne al’umma su yi iyakacin iyawarsu wajen dakile wannan mugun nufi, wanda zai iya jefa kasar nan cikin fishin Allah wanda hakan ka iya kara jefa kasar nan cikin mawuyacin hali fiye da wanda ake ciki.
” Wallahi idan muka bari wannan shirin nasu ya tabbata to zamu fuskanci fushin Allah, wanda Kuma bazai yiwa kowa dadiba Saboda a baya Allah ya hallaka da al’umma aka guda daga cikin laifukan da ake so a halasta a kasar nan, babu shakka muddin hakan ta tabbata to mu shirya shiga masifar da tafi wacce muke cikin yanzu “. Inji Sheikh Dauda Lokon makera
Daga karshe Sheikh Lokon Makera ya jaddada kkira ga al’umma da kungiyoyin addini da masu zaman kansu da su bada tasu gudunmawar wajen ganin an dakile wannan mummunan shirin wanda ka iya jefa Najeriya a cikin musiba.