Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar Talata, 25 ga Agusta, 2026, a matsayin ranar hutu ta kasa domin bikin ranar Maulidi, wato zagayowar ranar haihuwar Annabi Muhammad (SAW).
Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya sanar da hakan a madadin gwamnatin tarayya, cikin wata sanarwa da babbar sakatariyar ma’aikatar, Dr Magdalene Ajani, ta fitar a ranar Juma’a.

Tunji-Ojo ya taya Musulmi a Najeriya da mazauna kasashen waje murnar wannan rana, tare da kira ga ‘yan kasa da su yi tunani kan darussan tausayi, tawali’u da hidima ga al’umma da ke cikin rayuwar Annabi Muhammad (SAW).
Ministan ya ce bikin Maulidi wata dama ce ga al’umma ta yin tunani kan wadannan dabi’u da kuma yadda za a amfani da su wajen gina kasa mai zaman lafiya da hadin kai.
Ya kuma yi kira ga ‘yan Najeriya da su yi amfani da wannan lokaci wajen yin addu’ar samun zaman lafiya da hadin kan kasa, yana mai jaddada cewa kare hadin kan Najeriya nauyi ne da ya rataya a wuyan kowa.

Tunji-Ojo ya bukaci jama’a da su gudanar da bukukuwan cikin natsuwa da mutunta juna, tare da yi wa al’ummar Musulmi fatan yin Maulidi mai cike da farin ciki da zaman lafiya.
Ya kara tabbatar da aniyar gwamnatin tarayya na ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin al’umma tare da tabbatar da dorewar zaman lafiya a fadin kasar.