Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya buƙaci Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) da hukumomin tsaro da aka tura jihar Osun su tabbatar da gudanar da zaɓen gwamnan jihar cikin lumana, gaskiya da adalci.
A cikin wata sanarwa da mai ba shugaban ƙasa shawara kan yaɗa labarai da dabarun sadarwa, Bayo Onanuga, ya fitar ranar Juma’a, Tinubu ya ce INEC na da alhakin tabbatar da sahihancin tsarin zaɓen da kuma kare amincin sakamakonsa.

Shugaban ya buƙaci INEC ta yi amfani da zaɓen Osun a matsayin wata dama ta nuna shirinta na gudanar da babban zaɓen 2027 cikin inganci da gaskiya.
Haka kuma, ya umarci Rundunar ’Yan Sandan Najeriya da sauran hukumomin tsaro da aka tura jihar da su tabbatar da tsaron masu kaɗa ƙuri’a da jami’an zaɓe, tare da hana duk wani mai tayar da hankali kawo cikas ga zaɓen.

Tinubu ya ƙarfafa wa al’ummar Osun gwiwa da su fito su kaɗa ƙuri’unsu cikin ’yanci, ba tare da tsoro ko barazana ba.
Ya jaddada cewa sakamakon zaɓen dole ne ya kasance abin da ya dace da muradin al’ummar jihar, yana mai cewa sahihancin zaɓen zai dogara ne kan yadda sakamakonsa zai bayyana zaɓin masu kaɗa ƙuri’a.