Tsohon shugaban kungiyar ’yan Jarida ta Najeriya (NUJ) reshen Jihar Kano, Comrade Abbas Ibrahim, ya zama dan takarar mataimakin gwamna na Jam’iyyar Labour Party (LP) a Jihar Kano, gabanin babban zaben 2027.

Abbas Ibrahim ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce ya yanke shawarar yin murabus daga mukaminsa na Wakilin Amintattu na Kasa (National Trustee) na NUJ, Zone A, domin samun damar mayar da hankali kan sabon nauyin da aka dora masa.

Ya ce, “Cikin kaskantar da kai, godiya da kuma kishin abokan gwagwarmaya, ina sanar da ku cewa bayan na zama dan takarar mataimakin gwamna na Labour Party da aka sake tsara ta a Jihar Kano, na yanke shawarar yin murabus daga matsayina na National Trustee na NUJ, Zone A.”
Ya kara da cewa murabus din zai ba shi damar sadaukar da isasshen lokaci da kuzari wajen gudanar da wannan sabon nauyi tare da taka rawa sosai a harkokin siyasa.