Falakin Shinkafi, Amb. Yunusa Yusuf Hamza, ya ce alfarma ce babba mutum irin Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya kasance a cikinta.
Falakin Shinkafi ya bayyana hakan ne cikin sako taya sarki Sanusi II murnar cika shekaru 65 da haihuwa.

Ya ce Sarki Sanusi II mutum ne da yake da jajircewa wajen cimma burikansa, hakan tasa ya sami nasarori masu yawa a rayuwarsu.
“Da ya dauki harkar ilimin addini sai da ya kai makura, haka da ya fara ilimin boko sai sa ya zama Dr. Haka a harkarsa ta banki sa da ya zama gwamnan Babban Bankin Nigeria (CBN), don haka na ce shi na daban ne a cikin al’umma “. Inji Falakin Shinkafa

Falakin Shinkafi ya ce a sanadiyyar jajircewar Sarkin Kano Sanusi II jihar Kano da Nigeria sun sami cigaba musamman ta fuskar tattalin arzikin ta hanyar masu zuba jari.
Amb. Yunusa Yusuf Hamza ya ce a madadin ji kansa da iyalansa yana taya sarkin murnar cika wadannan shekaru masu tarin albarka.