Duk Wanda Ya San Sanata Barau, Ya San Ba Ya Son Rigima! Idan da gaske kana ƙaunar Sanata Barau I. Jibrin (Maliya), to ka yi koyi da halayensa.

Sanata Barau ba ya gina siyasa da zagi, faɗa ko ƙiyayya. Ya fi son zaman lafiya, haɗin kai, mutunta kowa da kuma aiki domin ci gaban al’umma.
Saboda haka, kada a yi amfani da sunansa wajen tayar da husuma ko cin mutuncin wani. Gaskiyar goyon baya ita ce nuna ɗabi’a ta gari, haƙuri da natsuwa kamar yadda jagoranka yake yi.

Mu yaɗa zaman lafiya, mu guji rigima, mu gina haɗin kai. Wannan ita ce hanyar Sanata Barau (Maliya).