Kotu Ta Dakatar Da Aikin BOA Plaza A Kano, Ta Umurci Manyan Jami’an Gwamnati Su Bayyana Gaban Ta

Date:

 

Babbar Kotun Jihar Kano mai lamba 11 da ke Bompai, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Justice Nasiru Saminu, ta sake umartar a dakatar da duk wani aikin ginin BOA Plaza da ke yankin Farm Centre, har sai an kammala shari’ar da ake yi kan mallakar filin.

Kamfanonin Jean B Project and Property Development Co. Ltd da G Empire Landmark Project Ltd ne suka shigar da ƙarar a gaban kotun, inda suka yi ƙarar hukumar tsara birane ta jihar Kano (KNUPDA) da Gwamnatin Jihar Kano.

Masu ƙarar sun yi zargin cewa an ƙwace musu filin da ake gudanar da aikin ba bisa ƙa’ida ba, tare da ci gaba da aikin ginin duk da cewa akwai takaddamar shari’a kan mallakar wurin.

IMG 20260704 WA0007
Talla

Lauyan masu ƙara, Barrister M. N. Duru, ya buƙaci kotu ta bayar da umarnin dakatar da aikin domin kare haƙƙin masu ƙara da kuma tabbatar da adalci kafin yanke hukunci na ƙarshe.

Sai dai lauyan KNUPDA da Gwamnatin Jihar Kano sun musanta zarge-zargen, inda suka bayyana cewa aikin yana gudana ne bisa tanadin doka.

Goyon Bayan Sanata Barau Na Ƙara Karfi a Kano Ta Arewa

Bayan sauraron hujjojin ɓangarorin biyu, Mai Shari’a Justice Nasiru Saminu ya bayar da umarnin dakatar da duk wani aiki a BOA Plaza daga ranar 30 ga Yuni, 2026, har zuwa lokacin da kotu za ta kammala sauraron shari’ar.

Kotun ta bayyana cewa dukkan ɓangarorin da ke cikin shari’ar, wakilansu da duk wani mai ruwa da tsaki, dole ne su kiyaye umarnin kotu tare da dakatar da duk wani aiki a wurin da ake takaddama.

A zaman kotun da aka gudanar ranar 7 ga Yuli, 2026, lauyan masu ƙara ya sanar da kotu cewa duk da umarnin dakatar da aikin, ana ci gaba da gudanar da gine-gine a BOA Plaza.

IMG 20260704 WA0005
Talla

Barrister Duru ya ce ci gaba da aikin bayan umarnin kotu na iya zama raina kotu, domin an karya umarnin da aka bayar.

Lokacin da Mai Shari’ar ya tambayi lauyan waɗanda ake ƙara game da wannan zargi, ya ce ba shi da masaniya kan ci gaban aikin.

Saboda haka, Mai Shari’a Nasiru Saminu ya umarci Sakataren Dindindin na ma’aikatar da abin ya shafa da kuma Babban Lauyan Gwamnatin Jihar Kano (Attorney General) su bayyana a gaban kotu a zama na gaba da aka sanya ranar 17 ga Yuli, 2026, domin bayar da bayani kan zargin ci gaba da aikin duk da umarnin dakatarwa.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnan Kano Ya Ƙaddamar Kwamitin Tsara Kundin Yaƙin Neman Zaɓensa a 2027

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya ƙaddamar...

Mutane huɗu sun maƙale bayan gini mai hawa biyu ya rufta a Kano

Mutane huɗu sun maƙale bayan wani ginin bene mai...

Goyon Bayan Sanata Barau Na Ƙara Karfi a Kano Ta Arewa

Yayin da ake ci gaba da tunkarar zaɓukan 2027,...

ADC ta rusa shugabancin jam’iyyar na Kano tare da kafa kwamitin riƙo

Jam'iyyar ADC ta rusa shugabancin ta na Jihar Kano...